Yadda alherin da jarumi Ali Nuhu ya yi wa wata mai tallar awara,ya taba zukatan jama'aDuk da irin suka da kahon zuka da aka kafa wa jaruma masana'antar Kannywood, a wasu lokoutan sun kan yi abun jinjina da yabo.l

Jaruman da suka fi samun yabo a wannan fannin sun hada da Hadiza Gabon, Ali Nuhu, Adam Zango da sauransu.

Abun alherin da jarumi Ali Nuhu ya yi wa wata mai tallar awara, ya taba zukatan jama'a

A nan jarumi Ali nuhu ne ya yi wani abun yabo da hali nagari da abokin aikinsa Abdul Saheer, wato Malam Ali na shirin Kwana Casa'in ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Me jarumin ya aikata?

Kamar yadda Abdul Saheer ya wallafa a shafinsa na Instagram, wani abokinsa ne ya bashi labarin abin kirkin da Ali Nuhun ya yi a kan idonsa . A cewarsa:

"Jiya nake hira da wani abokina sai ya ke ce min, Abdul Wallahi Ali Nuhu ya taba yin wani abu da ya taba ni. Sai na ke tambayarsa mene ne ya faru? Sai ya ce wata rana ya ga wata yarinya mai tallar awara tana kuka kan ta yi barin awarar ta, sai ga Ali Nuhu ya fito.

"Ya na zuwa ya ga yarinyar tana ta sharar kuka, nan take ya je har inda ta ke ya tsaya ya ke tambayarta shin mene ya ke faruwa da ke?

"Sai ta ce awarar ta ce ta bare, sai yace to daina kuka kin ji. Ya dauki kudi masu kauri ya ce ga wannan rike na baki duka, ki je amma fa ki daina kuka.

"Bayan Ali Nuhu ya shiga mota ya tafi, sai mutanen wajen suka ce wannan kudin da ya bai wa wannan yarinyar fa yanzu ya yi wani aiki voice over aka bashi. Ko aljihu bai saka kudin ba ya dauka ya ba wannan yarinyar.

"Abokina ya ce shi fa tun daga nan ya sallamawa Ali Nuhu a kan gaskiya wannan mutumin kirki ne. Muna alfahari da kai matuka @realalinuhu. Wannan shi ne ainihi ma'anar mutuntaka."

Wanne martani jarumin ya yi a kan wallafar?

Jarumi Ali Nuhun ya basi amsa da:

"Nagode, Allah yasa mu dace gaba daya."

Na yi sa'ar samunki: Ali Nuhu ya yada kyawawan hotunan bikin tuna ranar haihuwar 'yarsa

Jarumin ya bayyana a shafinsa na Instagram, inda ya yada wani kyakkyawan hotonsa da ‘yarsa tare da Fatima tare da bayyana irin sa’ar da ya samu da samun 'ya kamar ta.

Ali Nuhu ya yi magana cikin jin dadi game da bajintar Fatima kuma ya bayyana cewa ya yi sa’a da samun ta a matsayin ‘ya

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN