Allah Sarki: Nasiru Jatau mijin matar da jami'an tsaro suka kama a jihar Kebbi a 2019 bisa zargin tayar wa Gwamna hankali ta sms ya rasu


Allah ya yi wa Malam Nasiru Jatau rasuwa. Nasiru shi ne mutumin da jami'an tsaron DSS reshen jihar Kebbi suka kama tare da matarsa Aisha bisa zargin tayar wa Gwamnan jihar Kebbi hankali a wayar salula..

Malam.Nasiru ya rasu a Asibitin koyarwa na Usman Dan Fodio UDUTH a garin Sokoto sakamakon rashin lafiya ranar Alhamis 3 ga watan Fabrairu 2022.

Idan baku manta ba, ranar 1 ga watan Satumba 2019 da tsakar dare kuma ana cikin ruwan sama a garin Yauri, Jami'ai suka kutsa gidan Marigayi Nasiru Jatau suka kama mutum uku, wanda suka hada da shi kansa Malam Nasiru, Amaryarsa da kuma babban dansa aka saka su a cikin mota aka kai su Birnin kebbi aka tsare su domin gudanar da bincike.

An tsare su har tsawon kwana 13 ana gudanar da bincike, lamari da ya karasa a babban Kotun Majistare na jihar Kebbi karkashin Alkali Mungadi.

Daga karshe dai jami'an tsaro sun kasa gabatar da hujjojin kan zargi da tuhumar cin zarafin Gwamna kamar yadda suka tuhumi Malama Aisha Nasiru Jatau a gaban Kotu.

Daga bisani Kotu ta saki Aisha sakamakon gazawar jami'an tsaro wajen gabatar da hujjoji na tuhumar da suke yi mata a gaban Kotu duk da dage zanan Kotu har sau uku domin ba jami'an tsaro dama su gabatar da shaidu da hujja kan tuhumar da suke yi mata. Sakamakon haka Kotu ta ce ta sallami Aisha har sai ranar da jami'an tsaro suka kawo hujja na tuhumar da suke yi mata.

A matsayin Aisha Nasiru Jatau talakan jihar Kebbi ta fuskanci 

1 Tsarewa a Kurkuku duk da yake tana shayar da Jaririyarta yar wata biyar da haihuwa a waccan lokaci.

2. An tsare mijinta Marigayi Nasiru Jatau tare da babban dansu a hannanun jami'an tsaro.

3. Har yau an kasa tabbatar da hujjar abin da ya sa aka kama Malam Nasiru, Amaryarsa Malama Aisha da babban dan Nasiru Jatau.

4. Malam Nasiru Jatau ya rasa dama da ya samu na halartar intabiyu na samun damar zama shugaban Kwalejin fasaha ta jihar Kebbi da ke garin Dakin Gari, watau Kebbi state polytechnic.

5. Har yau ba a kammala biyan mahaifin Aisha hakkinsa na fansbo ba .

6. Malam Nasiru ya rasu ya bar wa wayanda suka cutar da shi Duniya lokacin da su suke neman Duniya da mulki ido rufe.

Ko amanar rayuwa zai sa ruhun Malam Nasiru ya hana makuntatansa samun kwanciyar hankali a Duniya?

Duba da yadda Amana ta fada wa wasu shugabannin al'umma da suka shude har da al'umman wannan zamani. Ba za a cire tunanin cewa amana za ta kama wadanda ke da hannu wajen kuntata wa Marigayi Nasiru Jatau tare da Matarsa Aisha ba.

Daradi da wasu shugabanni suka kasa ganewa saboda buguwa da giyar mulki shi ne, duk shugaba da ya yi kaurin suna wajen fada da talakawansa tare da wulakanta kimarsu, tabbas talaka ne ke zama sanadin faduwar daularsa tare da wanzar da karshen lamarinsa a doron Duniya.

Kwanta cikin rahamar Allah Malam Nasiru, Allah ya gafarta maka tare da dukkan Musulmi, Alllah ya hore maka Aljannah. Allah ya sa mu cika da Imani.


================

Daga Jaridar iyaku.com

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook fFacebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN