Abin da ya kamata ku sani game da zuriyar Dantata da ta fi dukiya a Afirka ta Yamma


Zuriya ce wadda ta shahara a bangaren kasuwanci ba kawai a Jihar Kano ko a Najeriya ba, har ma a fadin Afirka ta Yamma lura da yadda iyalan zuriyar suka fantsama don yin kasuwanci a duniya.

Wani abin tarihi game da wannan zuriya shi ne yadda suke gadar da harkar kasuwancin da suka gada kaka da kakanni, daga na gaba zuwa ga na baya.

Wannan ne ya sa har yanzu ake damawa da su a harkar kasuwanci ba kawai a Najeriya ba har da duniya baki daya.

Yanayin yadda suke gadar da dukiyarsu tun daga wanda ya kafa zuriyar Alhaji Alhassan Dantata ne ya sa ’ya’ya da jikokin zuriyar suka gaji kasuwanci da neman kudi, har ya kai ga a yanzu zuriyar gidan ta fi yawan masu dukiya a duk fadin Afirka ta Yamma.

Bincike ya nuna cewa duk da cewa ’ya’yan wanann zuriya suna yin karatun boko, inda a yanzu haka akwai wasu fitattu a banagrori da dama na ilimi amma mafi yawansu sun fi mayar da hankali ne wajen harkar kasuwanci.

Idan muka waiwaya za mu iya yin nazarin zuriyar daga zamani zuwa zamani.

Zamani na farko: Madugu Baba Talatin

Shi Madugu Baba Talatin falke ne wanda yana daga cikin iyalan ’yan kasuwar nan da ake kira da Agalawa wadanda suka dade una gudanar da harkar kasuwanci a al’ummar Hausawa da suke zaune a Katsina. Daga baya ya dauko iyalansa ya dawo Kano.

Shi Madugu ya shahara ne a bangaren kasuwanci rinannun tufafi da fataucin rakuma da harkar sayar da bayi da kuma goro. Ya rasu a garin Madobi da ke Jihar Kano.

Zamani na Biyu: Madugu Abdullahi

Madugu Abdullahi dan Madugu Talatin shi ma dan kasuwa ne mai dukiya wanda tun a wancan lokaci ya shahara a harkar kasuwancinsa kamar mahaifinsa.

Ya yi harkar fatauncin rakuma da na bayi idan kuma ya je fatauci yakan kawo ‘Wuri’ wanda shi ne kudin da ake kashewa kafin mulkin mallaka a kasar nan, idan Turawa sun kai shi kasar Ibory Cosat.

Haka kuma Madugu Abdullahi ya auri matarsa da ake kira da Maduga Amarya a 1877 inda suka haifi Alhassan.

A lokacin da ya rasu ’ya’yansa sun yi kankanta su iya tafiyar da dukiyar don haka aka rarraba musu gadon dukiyar kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

Bayan rasuwarsa sai matarsa ta bar ’ya’yan a hannun wata ’yar uwarta a garin Bebeji wacce ake kira Tata don ta ci gaba da kula da su inda kuma ta koma Accra Babban Birnin Kasar Ghana, ta zama babbar mai dukiya. Daga sunan wannan mata Tata ce Alhassan ya samu sunansa inda ake kiransa da “Dan Tata” .

Zamani na Uku: Alhassan Dantata

Alhassan Dantata bafatake ne kuma ya yi harkokin kasuwanci a Najeriya da kasashen Afirka. Daga baya sai ya zama babban dilan gyada inda yake kai wa Kamfanin Niger wanda daga baya ya zama Kamfanin UAC.

An ce shi kadai yake iya saye gyadar da Kamfanin UAC da ke Arewacin Najeriya yake tarawa. Kuma zuwa1922 sai ya zama babban dan kasuwa a Kano.

Lokacin da Bankin Ingila a Afirka ta Yamma ya bude ofishi a Kano a 1929, shi ne dan kasuwar da ya fara amfani da banki inda ya ajiye sulalla da dama. Lokacin da Alhassan Dantata ya rasu a 1955 shi ne dan kasuwa mafi dukiya a duk fadin Afirka ta Yamma.

Kafin rasuwarsa ya bar wasiyya cewa a raba wa matansa uku da ’ya’yansa dukiyarsa.

Zamani na hudu: Mahmud Dantata da ’yan uwansa

Mahmud Dantata wanda ka fi sani da Mahmud WAPA ya zama wanda ya gaji mahaifinsa inda ya ci gaba da gudanar da kasuwanicn mahaifinsa. Daga baya sai ya kafa kamfanin da ke jigilar alhazai a 1948 da ake kira da WAPA, da kuma kasuwar canjin kudade a Afirka ta Yamma.

Alhaji Aminu Dantata Yayin da mahaifin Alhaji Aminu wato Alhassan Dantata ya rasu sai ya zama Mataimakin Darakta a kamfanin mahaifinsa inda kuma yayansa Mamuda ya zama Manajan Darktan Kamfanin.

Bayan da Mahmud ya rasu a 1960 Alhaji Aminu Dantata ya zama Manajan Darkatan kamfanin, matsayin da yake rike da shi har zuwa wannan lokaci.

Wasu daga cikin kamfanonin da Alhaji Aminu Dantata yake jagoranta sun hada da Namco Nigeria Limited da Namco Technical Main Line Transport Ltd da Dantata Motors Ltd da Nigeria Sugar Products Ltd da Bebeji Oil Company da Dantata Inbestments and Securities Ltd da Dantata Properties Management Company Ltd da Edpress Petroleum Ltd da Fertilizer Processing Comapany Ltd da Kamfanin Agro Chemical da Kamfanin Associated Mining Industry Ltd.

Har ila yau Alhaji Aminu Dantata shi ne Shugaban Kamfanin Fulawa na Northern Nigeria Ltd da na Mansileta da Kamfanin Raleigh Industries Limited da kuma Kamfanin Unibersal Spinners Limited.

Haka kuma yana daga cikin jagororin Bankin Jaiz da Stallion Group da kamfanonin siminti da sauran kamfanoni masu yawa.

Sanusi Dantata Lokacin da Sanusi Dantata ya samu rabonsa na gado daga dukiyar mahaifinsa ya yi amfani da ita wajen farfado da harkokin kasuwancinsa na sufuri.

Zuwa 1990 Kamfanin Sanusi Dantata shi ne babban kamfanin da yake sayen gyada a Najeriya. Sanusi Dantata shi ne aka ce ya ba Aliko Dangote bashin da ya fara yin kasuwaci da shi kimanin shekara 30 da suka gabata.

A 1980 ya mayar da harkokin kasuwancinsa ga ’ya’yansa, har ma da babban dansa Abdulkadir Sanusi Dantata.

Lokacin da ya rasu an ce yana daya daga cikin masu kudi a Afirka ta Yamma. Abdulkadir Dantata Shi ne babban dan Sanusi Dantata.

Ya kafa Kamfanin Land and Sea, kamfanin da yake harkar sufuri da kerekere, inda daga baya ya zama cikakken kamfanin da a yanzu ake kira da Dantata & Sawoe da Asada Group da Kamfanin GineGine na Brunelli Construction Company da Kamfanin Goguwasia Trading Company Beijing-China.

Kasuwancinsa ya fi a harkar gine-gine da yin fiton kayayyaki da noma da kasuwanci. Usman Amaka Dantata A 1973 Usman Amaka ya tafi Legas don ya lura da harkokin kasuwancin mahaifinsa, inda cikin kankanin lokaci ya zama miloniya.

A kasa da shekara goma ya zama babba a harkar sufurin jiragen sama haka kuma ya zama cikkaken manomi kuma mai masana’antu.

A lokacin yana dan shekara 26, Usman Amaka tare da Yinka Folawiyo su kadai ne mutanen da Gwamnatin Soja ta Janar Murtala Mohammed ta sahalewa su rika shigowa da siminti daga kasashen waje.

Haka kuma a wancan lokaci duk da karancin shekarunsa ya mallaki wurin yin fito a tashar ruwa ta Apapa da ke Legas inda jiragen ruwansa ke zama.

Baya ga wannan kuma Usman yana da dukiya a kasashen waje musamman a kasar Birazil da kuma gonarsa da aka bayyana a matsayin gona mafi girma wajen samar da kaji a duk fadin Afirka ta Yamma wacce ke samar da kaji dubu 100 a kullum.

Amaka yana da jiragen sama na kashin kansa da suka hada da samfurin Boeing 707 wanda aka kawo shi daga Bistow.

Hajiya Mariya Sanusi Dantata

Ita ce mahaifiyar Attajirin Afrikan nan Alhaji Aliko Dangote kuma Shugabar kamfanoni da yawa da suka hada da Kamfanin Man fetur na MRS Oil Nigeria Ltd da Dangote Group.

Mata ce da ake girmamwa sakamakon ciyar da akalla mutum dubu biyar da take yi a kullum a Jihar Kano.

Alhaji Tajudden Dantata

Shi ne babban dan Alhaji Aminu Dantata kuma Manajan Darakta na Dantata Organisation. Haka kuma shi ke kare muradun kamfaninsu a kanmfanonin da suke da hannun jari irin su Electric Metre Company of Nigeria (EMCON) da Birgin Nigeria Airways da Mentholatum Nigeria Limited da Cement Company of Northern Nigeria.

’Yan uwansa suna taimaka masa wajen tafiyar da kamfanonin irin su Abubakar Saddik Dantata da Hassan Aminu Dantata da Aminu Dantata. Alhaji Nasiru Dantata Shi ne mutumin da ya kafa kamfanin lemo na Danta Cola a 1980.

Kuma shi ma yana da jirgin sama na kashin kansa.

Alhaji Sayyu Dantata

Sayyu Dantata ya fara aiki a matsayin Shugaban Sashen Zirga-Zirga na Kamfanin Dangote.

Daga baya ya zama Shugaban Kamfanin Mai na Chebron Oil Nigeria PLC.

Haka ya zama Shugaban Kamfanin Man fetur na MRS Nigeria PLC.

Sayyu wanda daya ne daga cikin mutum 20 mafiya kudi a Najeriya shi ne Daraktan Kamfanin Hydro Alternatibe Energy.

Alhaji Aliko Dangote

Alhaji Aliko Dangote dan Alhaji Muhammadu Dangote da Hajiya Mariya Sunusi Dantata. Jika ne ga zuriyar Dantata.

Aliko ya fara harkar kasuwanci da dan karamin kamfani a 1977 wanda a yanzu ya zama babban kamfani mai jarin tiriliyoyin Naira.

Kamfaninsa ya zama babban kamfani ko masana’anta a fadin Afirka ta Yamma kuma shi ne kamfani na uku a duniya wajen samar da siminti da fulawa da gishiri.

Haka kuma wannan kamfani yana kan gaba wajen shigo da shinkafa da taliya da kifi da siminti da takin zamani zuwa Najeriya.

An ce zuwa shekarar 2020 Aliko Dangote ya mallaki dukiya da yawanta ya kai Dalar Amurka biliyan 8.3 abin da ya sa ya zama na 162 a jerin masu kudin duniya kuma shi ne wanda ya fi kowa kudi a duk fadin Afrika.

A Janairun bana yana da dukiyar da ta kai Dala biliyan 14.1 kamar yadda Mujallar Forbes ta bayyana.

Dalilin da zuriyar Dantata ta fi dukiya a Afirka ta Yamma -Ibrahim Ado Kurawa

Da yake bayani kan dukiyar zuriyar ta Dantata, Dokta Ibrahin Kurawa wanda fitaccen masanin tarihi ne ya tabbatar da batun da ake yi cewa zuriyar ce mafi dukiya a Afirka ta Yamma Ya bayyana cewa abin da ya janyo Alhassan Dantata ya yi fice a cikin tsaransa ’yan kasuwa, shi ne yadda ya yi saurin karbar sabon tsarin kasuwanci na zamani.

“Bayan zuwan Turawa, da ya kasance Turawan ba yadda za su yi dole su dogara tare da yin hulda da ’yan kasuwa ’yan kasa da suka kawo harkar kasuwacin zamani sai ya karba. Ba kamar sauran mutane ko ’yan kasuwa da suka juya baya ga sabon tsarin ba.

“Alhassan Dantata ya shiga harkar saye da sayar da kayayyakin bukatu na yau da kullum, yana sayar musu kayayyaki yana aika musu da shi musamman gyada inda suka dauke shi a matsayin baban ejan dinsu na gyada a Kano musamman da yake a wancan lokacin Kano ce ke samar da gyada mafi yawa da ake kaiwa Turai,” inji shi.

Ya ce babban abin da ya kara kawo wa Alhassan Dantata karbuwa a wajen Turawa shi ne gaskiyarsa.

“Shi kasuwanci idan ba amincewa a ciki ba zai yiwu ba. Wanan kuma shi aka san Bahaushe da shi kafin abubuwa su fara rikicewa,” inji Kurawa.

Dokta Kurawa ya kara da cewa wani abu da ya kara daukaka Alhassan Dantata shi ne yadda ya zama kan gaba wajen kafa kamfanin ’yan kasa wanda ake kira Citizen Trading Company kamfanin da ya kafa masakar Gwammaja (Gwammaja Textile) wadda ita ce masaka ta farko a duk fadin kasar nan.

Dokta Ado Kurawa ya kara da cewa wani abu da ya kara sa zuriyar Dantata ta shahara shi ne yadda Alhassan Dantata ya yi wa ’ya’yansa tarbiyya tare da dora su a harkar kasuwanci tun suna kanana, “Ya tarbiyyatar da ’ya’yansa a kan harkarsa ta kasuwanci irin su Alhaji Sunusi Dantata da Mahmud Dantata aka zo kuma yanzu kan Alhaji Aminu Dantata wanda shi ne dansa da ya rage.

“Haka kuma zuriyar ta ci gaba da kyautata alakar gidansu da gwamnati da kuma ’yan boko da sauran ’yan uwansu ’yan kasuwa,” inji shi.

Mun kai 3,000 a yanzu – Hassan Dantata

Alhaji Hassan Sunusi Dantata jika ne ga Alhassan Dantata wanda jika ne ga Alhasan Dantata har ila yau kuma shi ne mai tattara duk wani tarihi da bayanan da suka shafi zuriyar Dantata, ya bayyana wa Aminiya cewa a kiyasi a yanzun zuriyar Dantat za ta kai mutum 3000.

“A gaskiya rabonmu da mu gudanar da kidayar zuriyarmu ta Dantata tun a shekarar 2016 inda muka samu yawan mutum dubu uku. Yanzu kin ga an shekara shida, to Allah ne kadai Ya san iya yawanmu, domin ni na san a duk mako sai an yi haihuwa a wannan zuriyar. Ka ga kuwa Allah ne Ya san iya yawan wadanda suka karu a cikinmu,” inji shi.

Ya bayyana cewa duk da canjawar zamani har yanzu mafi yawan ’ya’yan zuriyarsu sun fi yin harkar kasuwanci.

“Kasuwacin shi muka budi ido da shi, shi muka gada kaka da kakanni mafi yawa a cikin zuriyarmu harkar kasuwanci suke yi, ana dai samun kadan da suke aikin gwamnati. Wanan ba ya nufin ’ya’yanmu ba sa karatu, suna karatu.

“Akwai masu digiri ba ma daya ba har na uku amma za ka tarar kasuwancin nan dai shi suke yi. Wadanda suka yi karatu kamar na harkar lafiya za ka tarar suna aiki a asibitinmu da Alhaji Aminu ya gina,” inji shi.

Alhaji Hassan ya ce duk da cewa ba kowa ba ne a cikin zuriyarsu ya shahara wajen mallakar dukiya, amma yana da tabbacin cewa a cikin zuriyarsu babu talaka wanda yake cikin halin kaka-ni-ka-yi.

“Wani abin alfahari a cikin zuriyarmu shi ne duk da cewa ba dukkanmu muka yi suna wajen dukiya ba, amma a cikinmu babu wanda yake cikin talauci saboda a tsakaninmu akwai taimakekeniya. Mai shi yana taimakon wanda ba ya da shi don haka muke cikin rufin asiri.”

Ya ce zuriyar Dantata suna da biyayya a tsakaninsu “Wani abu da zuriyarmu ke da shi shi ne biyayya a tsakaninmu. Karami yana jin maganar wanda ke gaba da shi. Ko da mutum bai yi niyyar yin abu ba, idan wanda ya girme shi ya umarce shi ya yi, to zai yi ko da ba ya so, saboda biyayya.” inji shi.

Da aka tambaye shi ko zuriyar tana da wani asusu da ake taimaka wa ’ya’yan zuriyar sai ya ce duk da cewa suna da bukatu masu yawa lura da yawan mutanen da ke cikin zuriyar amma masu kudin sun gwammance su taimaka wa mutane a duk lokacin da bukata ta taso.

Ya ce, “Ganin cewa duk lokacin da abu ya taso masu kudin cikinmu sukan taimaka wa mabukatan da kudi masu dan kauri su gudanar da al’amuran da ke gabansu. Hakan ya sa ba mu fiye damuwa da yin asusun taimakawa juna ba.”

Rahotun Aminiya

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN