Abin da wani Kansila ya yi da karnuka a jihar Niger zai baka mamaki, duba ka gani


Kansila mai wakiltan unguwar Tudun Wada a karamar hukumar Chanchaga, Ibrahim Mai Farare, ya fatattaki jami’an Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Neja (NSEPA) da karnuka da yan daba kan gayyatarsa da aka yi ya zo ya amsa wasu tambayoyi.

Hukumar NSEPA dai na son ya amsa mata tambayoyi ne a kan wani wajen siyar da gas da yake kafawa a cikin unguwar.

Kansilan na fafatawa da yan unguwarsa ne a kan kafa wajen siyar da gas din

Mazauna unguwar sun yi kira ga gwamnati da hukumomin da abun ya shafa a kan su dakatar da shirin kafa wajen siyar da gas din, inda suka ce hakan hatsari ne a cikinsu.

Sun yi korafin cewa ana iya samun fashawar gas din duba ga cewar akwai harkokin kasuwanci da dama a yankin da ke bukatar wuta.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa a yayin da ta ziyarci yankin, ta gano cewa akwai masu suyan kosai, giajen gasa biredi da masu siyar tsire da dama a kewaye.

Domin kwantar da tarzoma, wasu jami’an Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Neja sun samu Kansilan da wasikar gayyata a makon jiya.

Amma sai karnuka suka kore su sannan yan baranda suka yi musu duka.

Kansilan ya tabbatar da lamarin a wani shirin radiyo na kai tsaye na Crusaders Radio a Minna.

Da aka tambaye shi game da lamarin a hirar, Kansilan ya ce:

“Eh, na kashe su, ba korarsu kadai nayi ba, kashe su na yi.”

Daya daga cikin mazauna yankin, Usman Galadima Mohammed, wanda ya kira a yayin hirar, ya kuma tabbatar da lamarin.

Ya ce yan daba sun yiwa jami’an NSEPA din mugun duka kafin karnuka suka kora su.

Wani babban jami’in NSEPA ya fada ma The Nation cewa hukumar ta kai kansilan kotu, inda ta bayyana shi a matsayin mai girman kai kuma bakauye.

Jami’in ya bayyana cewa babu wani amincewa na kafa gidan gas din a yankin.

Sai dai kuma, wasu mazauna yankin sun yi ikirarin cewa kansilan ba shine ainahin mai wajen gas din ba amma yana kare mai wajen ne bayan zargin cewa ya karbi N200,000.

Daya daga cikinsu, Annas Danlami, ya yi bayanin cewa mai wajen gas din ya ari wajen kan N500,000 da alkawarin cewa kayayyakin gas kawai zai siyar amma sai suka wayi gari suka ga ana kafa gidan siyar da gas.

Ya ce a lokacin da mutane suka nuna turjiya, sai mamalakin wajen ya fara jawo wasu kungiyoyi masu karfi da daidaikun jama’a domin neman yardarsu amma matasan yankin suka tsaya tsayin daka cewa ba za a kafa kamfanin ba.

Da aka tambaye shi a gidan rediyon ‘yan kan zargin karbar N200,000, sai Kansilan ya katse kiran.

'Yan bangan siyasan Matawalle sun kai mana farmaki a kotu, Hadimin Marafa

A wani labari na daban, sakataran yada labaran sanata Kabiru Garba Marafa na tsagin jam'iyyar APC a Zamfara, Bello Bakyasuwa, ya yi kira ga jami'an tsaro da su tsare musu rayukan su daga hare-haren da 'yan bangan siyasan Gwamna Bello Matawalle ke kai musu ba kakkautawa.

Bakyasuwa, wanda ya zanta da manema labarai bayan zaman da aka yi a babban kotun Gusau dake jihar Zamfara, ya koka game da yadda 'yan bangan siyasan Matawalle ke kai wa lauyan su da shi kanshi farmaki a cikin harabar kotun.

Inda yake bayyana cewa, ba wanda aka kama, ya yi kira ga jami'an tsaro da su tsaya bakin aikin su.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN