Yadda zaka kai korafi CBN idan Bankinka ya zalunce ka


Babban Bankin Najeriya, (CBN), ya fitar da matakan da kwastomomi za su shigar da korafin wani Banki da ya yi musu ba dai-dai ba, kuma wanda CBN ta amince su gudanar da kasuwanci a Najeriya.

Daily Trust ta rahoto cewa yayin sanar da matakan, CBN ya ce tun da farko ya umarci kowane Banki ya ƙara inganta sashin taimako na ATM, domin warware matsalolin kwastomomin su.

"Idan kana da wani ƙorafi kan Bankin da kake amfani da shi, wajibi da farko ka kai rahoton matsalarka a reshen Bankin da lamarin ya faru, sannan ka jira mako biyu (Ƙila ba zai kai haka ba) a warware matsalarka."

A cewar babban bankin, idan aka shafe mako biyu Bankin bai warware matsalar ba, to kwastoma na da damar kai korafinsa ga Daraktan sashin kare hakkin kwastomomi CPD.

Kwastoma na da damar tsallake Bankin sa bayan mako biyu, ya isar da ƙorafinsa ga babban bankin ƙasa ta sashin CPD, matukar Banki ya masa ba dai-dai ba.

Punch ta rahoto Sanarwan CBN tace:

"Kana da damar zuwa kai tsaye ka shigar da ƙorafinka ga CPD matukar Bankin kasuwancin da kake amfani da shi ya ƙi warware maka matsalarka cikin lokacin da aka ɗibar masa."

Ta ya mutum zai kai korafi CPD?

Haka nan kuma Bankin CBN ya bayyana yadda kowane ɗan Najeriya zai shigar da ƙorafin wani Banki kai tsaye ga sashin CPD na babban bankin Ƙasa.

"Za ka iya tuntubar sashin kwastoma CPD na Bankin CBN ta waɗan nan hanyoyin; Ofishin Sashin kwastomomi CPD dake Garki, babban birnin tarayya Abuja."

"Ka rubuta takardar korafi kai tsaye ga Daraktan CPD, ka sanya Adireshinsa. Kana da damar miƙa takardar korafin babban Ofishin CBN ko kuma kowane reshen CBN na ƙasa."

Yan fashi da makami sun farmaki motar dake ɗakko kuɗi ta Banki, sun kwamushe makudan kuɗaɗe a jihar Delta.

Rahoto ya nuna cewa yan fashin sun fasa motar da harsasan bindiga, yayin da suka ɗibi kudi suka yi gaba.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN