Tsakanin Bola Tinubu da al-ummar Arewa (Ra'ayin mai karatu)

Tsakanin Bola Tinubu Da Al-ummar Arewa




Daga Comr Abba Sani Pantami

A wannan lokaci da yankin mu na Arewacin Nijeriya mai albarka yake cikin tashin hankali, cikin halin damuwa, musamman abinda ya shafi rashin tsaro, talauci, rashin ilmi, da sauran su.

A wannan lokacin yankin Arewa yake buƙatar kulawar shuwagabanni, jajirtattu da za su bawa yankin kulawa don ganin mun fita daga cikin halin da muke ciki.

Duk wanda yake bibiyar siyasar Æ™asar nan, tun daga shekarar 1999 zuwa yau, irinmu da bamu da yawo labari kawai muka ji, yasan irin ta’asa da ta’annati da Tinubu ya yiwa al’ummar Arewacin Nijeriya, kamar yadda na rubuta a rubutuna da ya gabata, mai taken; ('Yan Arewa Za Su Yiwa Tinubu Hisabi Daidai Da Abinda Ya Aikata Musu) kuma babu wani wanda ya isa ya ce mana Tinubu yana son Arewa da ‘yan Arewa.

'Yan uwana 'yan Arewa mu tuna fa, su Tinubu ne fa suka Æ™irÆ™iri wata Æ™ungiya mai suna Oodua Peoples Congress" (OPC) a lokacin da yake gwamnan Jihar Legas, wannan Æ™ungiyar, duk shekara sai sun kashe ‘yan Arewa mazauna garin Legas, suka ware ranar June-12 na kowace shekara domin kisan gilla ga ‘yan Arewa mazauna Legas.

Ya kamata kusan cewa fa, Tinubu yana cikin waɗanda suka hana shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya buɗe iyakokin Arewa, domin su samu saukin rayuwa, shine ya tsaya tsayin daka domin ganin cewa sai dai a buɗe iyakokin Legas kawai, nufin sa anan shine, duk harajin da ake shigowa da kaya ya kasance sune kawai za su ci gajiyar abun, ban da 'yan Arewa.

Sannan duk mutumin da yake raye a Æ™asar nan, kuma yake bibiyar al’amurran gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, yana sane da cewa, su Tinubu sun amfana matuÆ™a da gwamnati mai ci, ko kuma muce sun fi kowa amfana, amma don rashin godiyar Allah, ku kalli yadda suka koma Æ™arÆ™ashin Æ™asa, suna yiwa gwamnatin bita da Æ™ulli, suna yi mata zagon Æ™asa.

Suka koma can a É“oye, suna zuga ‘yan iska da zauna gari banza, matasa marasa aikin yi, da shugabannin addinan yankunan su, waÉ—anda suka mayar da Addini abun wasa, waÉ—anda yawancin su ‘yan kudu ne, maÆ™iya yankin Arewa, suka koma suna yiwa wannan gwamnati tawaye da zanga-zanga.

Kowa yasan da cewa wasu hamshaÆ™ai ne suka É—auki nauyin zanga-zangar #END SARS a shekarar 2020 da ta gabata, kuma ba komai yasa suka yi wannan ba, sai don su tozarta gwamnatin Muhammadu Buhari, kuma su tozarta Arewa da ‘yan Arewa, wannan shine kawai manufar su, kuma duk suna yi ne domin maganar siyasar 2023, wato dole idan Buhari ya gama ya miÆ™a musu mulki da Æ™arfi da yaji, saboda haka muke Æ™ira ga ‘yan Arewa da mu farka, mu san irin Æ™ulle Æ™ulle, da makircin da ake Æ™ulla mana.

A wannan lokacin da mu 'yan Arewa muke cikin kuka, da addu’o’i, da Æ™oÆ™arin nemo mafita, da Æ™oÆ™arin Æ™ira ga shugabanni, su nemo hanyoyin magance waÉ—annan matsaloli da suka addabe mu, a lokacin ne kuma wasu lalatattu, gurbatattu, marasa kishi daga yankin Arewa, waÉ—anda da ma can su ba Arewar ce a gaban su ba, a’a, kawai su me zasu samu, me kuma zasu sawa aljihunsu, shine kawai a gaban su, waÉ—annan mutane, ina mai yi maku rantsuwa da Allah, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi kaÉ—ai, kuma baya da abokin Tarayya, kuÉ—i kawai ne a gaban su ba Arewa da ‘yan Arewa ba.

Daga cikin su akwai wasu ‘yan siyasa daga yankin Arewa, akwai wasu gwamnoni daga Arewa, akwai wasu sarakuna daga yankin Arewa, akwai wasu malaman addini daga yankin Arewa, akwai wasu matasa daga yankin Arewa, akwai wasu ‘yan kasuwa daga yankin Arewa, da dai sauran É“angarori na mutane, wanda a yanzu haka wasu sun fara bayyana kansu, to sune wai suka hadu, suka sha alwashin sai sun Æ™ara kassara Arewa, sai sun Æ™ara durÆ™usar da Arewa, sai sun sayar da ‘yanci da mutuncin Arewa, da wasu ‘yan kuÉ—i da zasu sa aljihunsu, ko kuma su cika asusun ajiyar su na bankuna.

WaÉ—annan mutane, kamar yadda muke da tabbaci, zasu yi amfani da sarakuna, zasu yi amfani da Addini, zasu yi amfani da Æ™ungiyoyin Addini, zasu yi amfani da malaman Addini, zasu yi amfani da wasu matasa, su basu kuÉ—i, su saye su, domin su cimma mummunan burin su na cin amanar Arewa da ‘yan Arewa.

A lokacin da su Sunday Igboho, Dokubo Asari, Ganiyu Adams, Nnamdi Kanu da sauran ‘yan iska, da ‘yan daba, ire-irensu, da Æ™ungiyoyi waÉ—anda aka kafa su domin yakar Arewa da ‘yan Arewa, irin su Amotekun, suke yiwa Arewa da ‘yan Arewa barazana akan dukiyoyinsu da rayukansu, ta kowane É“angare, sannan kuma suke kai hare-hare, iri-iri, ga ‘yan uwan mu da ke zaune a yankin kudu, babu wani babba daga cikinsu da ya tsawata musu, bamu ji wani babba daga cikinsu yayi Allah waddai da wannan irin cin mutunci da aka yiwa ‘yan uwan mu ba.

A wannan yanayi da muke cikin ne waÉ—annan gurbatattu, marasa kishi, wai zasu dauko Bola Tinubu, domin ‘yan Arewa sun goyi bayansa, ta Æ™arfi da yaji, waÉ—annan mutane su kawai, ba matsalar Arewa ce a gaban su ba, ba ‘yan uwansu da ake sacewa, ko ake kashewa kullum ne damuwar su ba, a’a, su damuwarsu ita ce, dole sai sun sayar wa da ‘yan Arewa Bola Tinubu, Dole sai sun sa ya samu karÉ“uwa a Arewa.

'Yan Arewa sun ce basa son wannan mutumin, sun ce basa ra’ayinsa, sun ce ba shida wata manufa ta Alkhairi gare su, sun ce sun haÆ™ura kawai da wannan mutumin, sun fada muku gaskiya, amma waÉ—annan mutane sun dage, sun sha alwashi, wai ko muna so, ko bamu so, sai sun Æ™aÆ™aba mana Tinubu da Æ™arfi da yaji.

Sannan ‘yan uwana talakawa ‘yan Arewa, ina kira da ku yi karatun ta natsu, wallahi kar ku yarda Tinubu ya samu karÉ“uwa a Arewa ta ko halin Æ™aÆ™a, ku bar shi ya gama yawace yawacen yawon kamfen É—in shi a banza.

Wallahi ba nayi wannan rubutun bane domin cin mutuncin wani ko kuma farantawa wani rai, a’a, nayi ne domin kishin Æ™asa ta Nijeriya mai albarka, da kuma kishin yankina na Arewa mai daraja, tare kuma da Æ™oÆ™arin bayar da gudumawa wurin samar da shugabanci nagari, wanda kowa zai ji dadi a cikinsa, ba shugabanci irin na ‘yan jari hujja ba. 

Kuma wannan ra’ayina ne, sannan ban hana kowa É—aukar ra’ayinsa sabanin wannan ba, amma dai muna da yaÆ™inin cewa, gaskiya muke faÉ—a muku, kuma tsakaninmu da Allah, kuma ita gaskiya, É—aci gare ta, sannan daga Æ™inta sai É“ata.

Sannan don Allah ina roÆ™onku, idan mutum yana son ya Æ™ara sanin ko waye Bola Tinubu, to yayi Æ™oÆ™ari ya nemi Khudubar Jumma’ah, wadda Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, ya gabatar a lokacin da Æ™ungiyar yarbawa zallah ta OPC tayi wa ‘yan uwan mu ‘yan Arewa kisan gilla, a Legas da Shagamu da sauran wurare.

Daga Æ™arshe, ina roÆ™on Allah ya bamu shugabanni na gari a zaÉ“e mai zuwa, ya taimaki Æ™asarmu Nijeriya, Allah ya taimaki Arewacin Nijeriya, ya hore mana lafiya, da zaman lafiya, da cigaba mai É—orewa, mai amfani, kuma ina rokon Allah yasa ‘yan uwana mu gane gaskiya, kuma ya bamu ikon bin ta, kuma Allah yasa mu gane Æ™arya da yaudara, kuma ya bamu ikon guje mata, Amin.

Don haka yanzu ya rage namu, shin zamu bari ayi amfani da mu? 

Shin zamu bari wasu marassa kishi, su lalata muna yanki, saboda biyan bukatar su?

Comr Abba Sani Pantami

NB: Wannan ra'ayin marubucin ne ba ra'ayin Jaridar isyaku.com ba.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakulabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN