Fasto ya rabo matar aure da 'ya'yanta mata 2 daga gidan miji, ya kawo su gidansa yana lalata da su a Ogun


Faston Cocin Spirit-Filled International da ke Olomore a Abeokuta, Timothy Oluwatimilehin yana hannun Rundunar ‘Yan sandan Jihar Ogun bisa zargin sa da yaudarar wata mata da yaranta biyu inda ya ke lalata dasu bayan zuga matar wurin barin gidan mijin ta, The Nation ta ruwaito.

Mijin matar, wanda ya kasa ceto matarsa da yaran nasa guda biyu daga hannun Fasto Oluwatimilehin akan lalatacciyar alakar da ke tsakanin su, ya samu taimakon ma’aikatar harkokin mata ta Jihar Ogun, inda suka garzaya ofishin ‘yan sanda da ke Adatan don kai korafi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya sanar da manema labarai hakan a ranar Alhamis.

DSP Oyeyemi ya ce DPO din Ofishin ‘yan sanda na Adatan, SP Abiodun Salau, ya tura yaran sa don su kama faston.

Ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce wanda ake zargin ya amsa duk laifukan da ake zargin sa da aikatawa.

Kamar yadda Tribune ta ruwaito, Kakakin ya ce:

“Faston ya amsa laifukan inda ya bukaci a yafe masa. Yayin bayanin ya ce ya yi amfani da damar fadan da matar suka yi da mijinta wurin shiga tsakanin su don ya yi lalata da matar.

“Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Lanre Bankole ya umarci jami’an yaki da satar mutane da bautar da kananun yara na bangaren binciken sirri don su ci gaba da bincike akan lamarin kuma suyi gaggawar gurfanar da mai laifin kotu.”

Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN