Murna a jama'ar Zamfara bayan soji sun yi wa Yan bindiga dagargazar Allah kara a cikin daji


Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar ragargazar ‘yan bindiga a sansanin su da ke Gwashi, karamar hukumar Bukkuyum da wasu bangarori na dajin Anka da ke jihar Zamfara inda suka amso shanaye da dama
.

Gidan Talabijin din Channels ya tattaro bayanai a kan yadda ‘yan bindiga suka yi kawanya a dajin Gando inda sojin suka zagaye su suka halaka yawancin su.

Mazauna kauyakun da ke kusa sun bayyana suna shagulgula a kan nasarar da sojojin suka yi yayin karon su da ‘yan bindigan.

‘Yan bindigan sun dade suna amsar haraji daga hannun mazauna karamar hukumar Bukkuyum tare da barazanar ganin bayan su matsawar ba su biya ba.

Har wasika ‘yan bindigan suka tura wa garuruwan Wawan Icce Salihu, Wawan Icce Ibrahim, Gangara, Gande, Tungar Gebe, Galle, Nan Narki, Ruwan Kura da ‘yar Galma da ke karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.

A farkon watan Janairu, ‘yan bindigan su kai wa wasu kauyaku 4 farmaki a karamar hukumar Anka da Bukkuyum inda suka halaka fiye da mutane 50, Channelstv ta ruwaito.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alawadai a kan kisan a lokacin sannan ya lashi takobin ganin bayan ‘yan bindigan.

“Yan bindigan nan za su zama tarihi, ba za mu zauna ba har sai mun ga karshen ‘yan ta’addan da suka addabi mutanen gari, suna halaka wadanda basu ji ba basu gani ba,” a cewar Buhari a lokacin.

“Muna bukatar jama’an da harin ya shafa su kara hakuri yayin da muke mika ta’aziyyar mu ga ‘yan uwan wadanda lamarin ya shafa. Mun jajirce wurin ganin bayan duk wasu ‘yan ta’adda don kawo zaman lafiya a kasar nan.”

Daraktan yada labarai, Bernard Onyeuko, ya sanar da hakan yayin bayar da bayani kan ayyukan sojojin a ranar Alhamis a Abuja, Premium Times ta ruwaito.

Onyeuko ya ce sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun halaka 'yan ta'adda 37, sun cafke 17 tare da samo miyagun makamai 117.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN