Hukumar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta sanar da cafke wani mutum mai suna Ali Lawan mazaunin karamar hukumar Kirfi bisa zargin yi wa ‘yar cikinsa mai shekaru uku a duniya fyade wato Hajara Lawan a ranar 9 ga watan Janairun 2022.
A cikin wata sanarwar manema labarai da kakakin rundunar SP Ahmad Mohammed Wakil ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewar duk a wannan ranar, matar wanda ake zargi Maryam Abdullahi ta kai rahoton faruwar lamarin ga shalkwatan ‘yan sanda da ke Kirfi.
Maryam Abdullahi, matar aure mai shekara 24 a duniya da ke zaune a unguwar Doya da ke karamar hukumar Kirfi ta kai korafin mijintta ga ‘yan sanda tare da cewa shi ‘Ali Lawan’ ya bukaceta da ta kawo masa tabarma don ya kwanta kawai sai ya hayake wa diyarsa Hajara kafin ta dawo.
“Ta dawo daga cikin dakin sai ta tarar da Hajara kwance a sume tana amai ta hanci da baki kuma al’aurarta ya kumbura.”
SP Ahmad Wakil ya kara da cewa, wacce tsautsayin ya faru da ita an garzaya da ita zuwa babban asibitin Kirfi domin nema mata kulawar likitoci na gaggawa inda likitocin suka tabbatar da cewa ‘an mata fyade da karfin tsiya’.
Tunin ‘yan sandan suka sanar da cewa sun kame wanda ake zargi (mahaifin Hajara) kuma bincikensu na cigaba da gudana a halin yanzu, “Za mu gurfanar da shi a kotu da zarar mun kammala bincike,” inji Wakil.
Har-ila-yau, ‘yan sandan sun kuma sanar da cewa sun samu nasarar kama wani mutum mai suna Ya’u Haruna dan shekara 25 da ke kauyen Lim ta garin Bununu a karamar hukumar Tafawa Balewa a ranar 13 ga watan Janairu bisa zarginsa da hada kai da wasu uku (da ake nema a halin yanzu) inda suka yi garkuwa da wani mutum mai suna Musa Adamu da ke kauyen Jambil a karamar hukumar.
Ya ce, sun samu bindiga kirar gida a hannun wanda suke zargi tare da alburushi, kana ya ce sun aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Disamban 2021, inda suka nemi fansar N8,000,000 kafin su sake wanda suka yi garkuwa da shi, “A wajen amsar kudin ne aka kama shi,” inji ‘yan sanda.
Dukka cikin nasarorin da suka samu a wannan watan, Wakil, ya kara da cewa a ranar 13/01/2022 jami’ansu sun samu nasarar kama wani mai suna Adamu Musa dan shekara 27 a duniya da ke kauyen Sabon Garin Batal, Tafawa Balewa bisa zargin yin garkuwa da wani yaro ‘Shuaibu Abdulkarim’ mai shekara 15 a duniya biyo bayan shiga gidan Abdulkarim Lawan da suka yi a ranar 10/1/2022 a kauyen Gamu.
“Wanda muke zargi Adamu Musa ya amsa laifinsa da kansa kuma ya bayyana sunan mutum bakwai da ya ce sun yi tarayya wajen aikata wannan laifin amma su har yanzu ba a kama su ba tukunna kuma bincike na cigaba da gudana.”
Sanarwar ta ‘yan sanda ya kuma kara da cewa, a 11/01/2022 sun kama wani Abdulrahman Isma’il mai shekara 25 bisa zargin garkuwa da wani yaro dan shekara biyar mai suna Aminu Isma’il a hanyarsa ta dawowa daga makaranta inda ya nemi fansar naira miliyan daya.
PPRO Wakil ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Umar Mamman Sanda ya gargadi masu aikata munanan laifuka da cewa su gaggauta sauya tunaninsu domin kuwa ba za su barsu suna cigaba da aikata munanan ayyukan ta’addanci a jihar ba.
Ya ce dukkanin wadanda suka kaman za su gurfanar da su a gaban kotu da zarar suka kammala bincike, inda suka nemi jama’a da su cigaba da taimaka musu da rahotonnin bata-gari domin daukan matakan da suka dace.
Leadership Hausa
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari