Girma ya fadi: Yadda wata Jaruma ta dambace direban tasi a bainar jama'a saboda kudin mota (Bidiyo)


Jarumar birnin Accra na kasar Ghana "Kylie Jenner'' ta dambace wani direban tasi sakamakon jayayya kan farashin tasi.

Takaddama ta tashi ne bayan direban tasi da ake kiransu "Yango" ya gaya wa Jarumar adadin kudi da ya kamata ta bashi bayan ya kai ta wajen da za ta je.

Sai dai Jarumar ta yi zargin cewa direban tasi ya zura kudi fiye da kima, sakamakon haka ta bashi adadin kudi da take ganin sun cancanta a ra'ayinta.

Direban tasi ya ki ya karbi kudin, kuma ya dage a kan cewa sai fa ta bashi cikakken kudinsa.

Bisa wannan dalili ne dambe ya kaure tsakanin Jaruma da direban tasi.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN