Duba sabuwar ayabar da ka iya ciyar da miliyoyin mutane a Afirka


Masana kimiyya sun ce wani ɗan itace mai suna enset, wanda abinci ne a Habasha wato Ethiopia, zai iya ceto al'ummar duniya yayin da ake fama da matsalar sauyin yanayi.

Ɗan itaciyar mai kama da ayaba ka iya ciyar da mutum miliyan 100 a duniyar da ke ƙara ɗumama, a cewar wani bincike.

Ɗan itaciyar bai shahara ba a wajen Ethiopia, inda ake yin fatensa kuma a yi burodi da shi.

Binciken ya nuna cewa za a iya shuka itacen a yankuna da dama na Afirka.

"Wannan itace ne da zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo ƙarshen matsalar abinci da kuma ɗorewar rayuwa," a cewar Dr Wendawek Abebe na Jami'ar Hawassa da ke Awasa, Ethiophia.

Itaciyar Enset ko kuma "ɓarauniyar ayaba" dangin ayaba ne amma a wani ɗaya kawai ake amfani da shi a Ethiophia.

Ba a iya cin ɗan itaciyar amma ana iya amfani da shi wajen yin fate-fate sannan kuma a yi burodi.

Enset wani abinci ne a Ethiophia, inda mutum kusan miliyan 20 suka dogara da shi, amma ba a nomansa a sauran wurare - duk da cewa akwai danginsa da ba za a iya ci ba - a kudancin Afirka, abin da ke nufin za a iya shuka shi a wuri mai nisa.

Ta hanyar amfani da jin ra'ayi da kuma bincike, masana kimiyya sun ƙiyasta amfanin enset cikin shekara 40 mai zuwa.

Sun gano cewa itacen zai iya ciyar da mutum miliyan 100 kuma ya haɓaka samar da abinci a Ethiophia da sauran yankunan Afirka, ciki har da Kenya da Uganda da Rwanda.

"Yana da wasu abubuwa da ba a saba gani ba a 'ya'yan itatuwa," in ji Dr James Borrell na Royal Botanic Gardens da ke Kew.

"Za a iya shuka shi kuma a girbe a kowane lokaci, kuma yana da tsawon rayuwa. Shi ya sa suke kiran sa da bishiyar kare yunwa."

Ethiophia ƙasa ce da aka sani da itatuwa iri-iri a Afirka, kamar gahawa da sauransu.

Ana tsammanin sauyin yanayi zai iya shafar hanyoyin samar da abinci a faɗin Afirka da sauran sassa.

Ana ci gaba da samun yunƙurin nemo wasu 'ya'yan itatuwar don ciyar da duniya, ganin yadda muka dogara da itatuwa marasa yawa. Kusan rabin abubuwa masu gina jiki da muke ci muna samun su ne daga dangin hatsi uku - shinkafa da alkama da masara.

"Akwai buƙatar mu faɗaɗa hanyoyin itatuwa a duniya saboda a yanzu abubuwan namu ba su da yawa," a cewar Dr Borrell.

An wallafa binciken ne a Environmental Research Letters.

Rahotun BBC Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN