Duba jerin Sunaye: Rundunar sojin kasa ta yi girgiza, an sauya wa GOCs da manyan hafsoshi


Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya, ya amince da nadi tare da sauya wa manyan sojojin kasa wuraren aiki duk don ba su kaimin yaki da ta’addanci a kasar nan. 

A wata takarda wacce darektan hulda da jama’an soji, birgediya janar Onyema Nwachukwu ya saki a Abuja, ya ce wadanda lamarin ya shafa ya hada da kwamandoji da sauran manyan sojoji, Daily Nigerian ta ruwaito hakan. 

Sauran wadanda abin ya shafa sun hada da kwamandan Kwalejin yaki ta sojojin Najeriya, Manjo Janar Solomon Udounwa wanda yanzu ya koma shugaban shirin sojoji na musamman a sabuwar Hedkwatar ayyuka na musamman na sojoji. 

A cewarsa, an mayar da Manjo Janar MT Durowaiye daga hedkwatar sojoji ta tsare-tsare da shirye-shirye zuwa hedkwatar soji da kuma darektan harkokin tsofaffin soji. 

Manjo janar AE ya koma Hedkwatar bangaren tsare-tsaren soji zuwa bangaren horarwar sojoji a matsayin darektan ayyukan tsaro yayin da Manjo Jamar UT Musa ya koma hedkwatar runduna ta 81 a matsayin kwamanda. 

Manjo Janar CU Onwunko ya koma darektan sadarwa na DHQ; Manjo Janar OO Oluyede ya koma Hedkwatar runduna ta 6 a matsayin kwamanda da kuma Manjo Janar LT Omoniyi ya koma hedkwatar rundunar soji na ayyuka a matsayin darektan tsare-tsare,” a cewarsa. 

Mr Nwachukwu ya kara da bayyana yadda aka tura Manjo Janar OJ Akpor daga NDA zuwa hedkwatar tsaro a matsayin darektan labaran soji, yayin da aka mayar da Manjo Janar Abdulwahab Eyitayo ya koma runduna ta 6 zuwa hedkwatar tsaro a matsayin darektan tsare-tsare. 

Ya kara da cewa, an mayar da Manjo Janar LA Fejokwu ya koma darektan tantancewa da tabbatar da tsari na DHQ, Manjo Janar JAL Jimoh ya koma makarantar sojoji ta Artillery zuwa hedkwatar horarwa ta TRADOC a matsayin shugaban horarwa. 

Ya ce manjo janar HT Wesley ya bar ofishin shugaban rundunar sojin kasa zuwa hedkwatar labarun sirri na soji a matsayin darektan ayyuka, sai manjo janar JO Ochai ya koma makarantar sojoji ta Armour a matsayin kwamanda. 

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, ya kara da cewa an mayar da manjo janar SG Mohammed bangaren tsaro da ayyuka a matsayin mataimakin shugaba daga runduna ta 6 ta sojin Najeriya da sauransu. 

Cikin sauran wadanda abin ya shafa sun hada da birgediya janar AS Maikano ya koma kwamandan bangaren kudi a asusai daga bangaren inshora na walwalar soji. 

“Birgediya janar LA Lebo ya zana zama mataimakin shugaban horarwa (Linkages/Integration) yayin da Birgediya janar MO Ihanuwaze ya koma darekta na kasafi da asusai (AHQ) da kuma birgediya janar Ojogbane Adegbe ya koma darektan Psychological Operation, fannin AHQ na harkokin Fararen hula da soji,” a cewar Nwachukwu. 

Kakakin sojin ya bayyana yadda shugaban rundunar tsaro ta kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya, ya hori duk wadanda aka nada a sababbin mukamai da su jajirce su kara dagewa wurin yin ayyukansu. 

A cewarsa, COAS din ya yi kira gare su da su kasance masu yin ayyukansu yadda ya dace. 

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN