Da duminsa: Gini ya ruftawa masu ibada sun mutu ana tsakar bautar Allah, duba yadda ta faru


Ginin cocin Housing Salvation dake Okpanam, karamar hukumar Oshimili ta arewa a jihar Delta, ya kife kan mutane suna cikin ibadar Allah.

 Jaridar Vanguard ta rahoto cewa har yanzun ba'a gano adadin yawan mutanen da Cocin ta danne ba, amma an zaro gawarwakin aƙalla mutum 10. 

Ginin cocin, wanda rahotanni suka tabbatar da yau ne karo na farko da aka fara amfani da shi, ya rushe ne da misalin ƙarfe 5:55 na yammacin ranar Talata. 

Rahotanni sun bayyana cewa masu aikin ceto sun zaro mutum takwas da ba su ji rauni ba, yayin da aka gaggauta kai wasu mutum hudu asibitin Asaba Special. 

Sakataren fadar gwamnatin jihar Delta, Chief Patrick Ukah, kwamishinan lafiya, Dakta Ononye Mordi, sun dura wurin da lamarin ya faru.

 A yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton, jami'an agaji na Red Cross da Jami'an kwana-kwana sun isa wurin domin cigaba da aikin ceto mutanen da lamarin ya rutsa da su. 

Karin Bayani na nan tafe... 

Source: Legit.ng 

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN