Dattiijo ya yi wa Gwamnatin Kebbi kaca-kaca kan matsalar rusau a shiyar Zabarmawa a garin Birnin kebbi(Bidiyo)Wani Dattijo a shiyar Zabarmawa da aka rushe gidansa, ya zargi Gwamnatin jihar Kebbi da aikata rashin adalci wajen gudanar da rusau a shiyar. Shafin isyaku.com ya samo.

Malam Abdullahi ya ce " Duk gidana gaba daya N1.4.m aka bani, yanzu wata guda kenan da bani kudi. Ko Gwamnati bata inya Gina gida a cikin wata guda, domin ga gida can ga Gwamnati shekaru nawa bata kare su ba.

" Za mu barsu ga Allah, ba ka iya fada da Gwamnati tunda ba Gwamnatin kwarai ce ba, ba Gwamnatin adalci ce ba. Abin da ake so ga Gwamnati, ai akwai inda muke ji ana basu kudi a basu fili da isashen lokaci su yi gini.

Amma ba kudi da za su yi maka gini, ba lokaci. Yau fili kawai in kana bukata sai ka saye shi Naira miliyan daya da wani abu". Inji Malam Abdullahi

Malam Abdullahi ya ce yana da dakuna hudu a gidanshi bayan ban daki da wajen dafa abinci da haraba. Ya yi korafin cewa N1.4m da Gwamnati ta ba shi bai isa ya saye fili kuma ya yi gini a cikin wata daya ba, kafin aka gudanar da rusau da ya yi sanadin rushe gidansa.

Kalli bidiyo:


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakulabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN