Wasu miyagun yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun yi awon gaba da, Jephthah Robert, ɗan uwan tsohon shugabn ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan.
Jaridar Punch ta rahoto cewa maharan sun sace shi ne a kofar gidansa ranar Talata da misalin ƙarfe 9:30 na dare a kusa da hanyar Dimrose, Yenagoa, jihar Bayelsa.
Shugaba kuma mamallakin kamfanin Zeetin Engineering Limited, Azibaola Robert, ƙani ne ga wanda yan bindiga suka sace kuma yan uwa ga Jonathan.
Shin yan sanda sun samu rahoto?
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata gajeruwar sanarwa da ya fitar.
Butswat ya ce:
"Maharan sun ɗauke shi ne a kan hanyar Dimrose dake Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa. Tuni muka fara kokarin kubutar da shi da kuma kama masu garkuwan."
"A halin yanzun muna aiki tukuru kuma da alamun nasara a kokarin ceto shi."
An sako kwamishinan jihar Bayelsa
Garkuwa da ɗan uwan Jonathan na zuwa ne awanni 24 bayan kwamishinan cinikayya da kasuwanci na jihar Bayelsa, Federal Otokito, ya kuɓuta daga hannun yan bindiga.
Mahara sun sace kwamishinan ne ranar 20 ga watan Janairu, 2022 a cikin gidansa dake ƙauyen Otuokpoti, ƙaramar hukumar Ogbia, jihar Bayelsa.
Ya kwashe kwanaki biyar a sansanin waɗan da suka yi garkuwa da shi, kafin daga bisani su sako shi ranar Litinin.
Wasu miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari na rashin imani ƙauyen Bobi, dake ƙaramar hukumar Mariga a jihar Neja.
Rahoton da The Nation ta tattara ya bayyana cewa maharan sun kashe dandazon mutane da har yanzun ba'a gano adadin su ba.
Source: Legit.ng
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakulabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI