Yan bindiga sun kone bas cike da mutane a Mali


Mutane akalla 31 ne suka mutu a Mali yayin da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan wata mota kirar bas, da ke dauke da farar hula a lokacin da take kan hanya zuwa wata kasuwa a tsakiyar kasar.

Hukumomin kasar ta Mali sun bayyana cewa 'yan bindigar da ba a san su ba sun bude wuta ne a kan motar inda suka kashe direbanta kafin kuma su cinna mata wuta da fasinjoji a ciki.

Motar dai tana zuwa kasuwar ne sau biyu a mako, daga kauyen Songho zuwa wata kasuwar da ke kauyen Bandiagara, wanda ke da nisan kilomita goma daga inda take tasowa.

Bayanai sun ce yawancin mutanen cikin motar mata ne da ke zuwa cin kasuwar tare da yara, akwai ma masu juna biyu da tsofaffi.

Lamarin ya faru ne a yankin Mopti, daya daga cikin yankunan da ake samun yawaitar hare-hare da ke da alaka da masu tayar da kayar baya wadanda ake dangantawa da Al-Qaeda da kungiyar IS.

Mummunan harin shi ne na baya-bayan nan a hare-haren masu ikirarin jihadi a kasar ta Mali.

Magajin garin Bankass, kusa da inda aka kai harin ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, 'yan bindigar sun bude wuta a kan bas din, sannan suka yayyanka tayoyinta, kafin kuma su rika harbin mutanen da ke cikin motar.

Ya ce akwai wasu karin mutanen cikin motar wadanda ko dai sun bata ko kuma an raunata su.

Wasu hotuna masu tayar da hankali da aka rika sanyawa a shafukan intanet, sun nuna motar kone cike da gawarwaki, sai dai BBC ba ta tabbatar da sahihancin hotunan ba.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto gwamnatin rikon-kwarya ta Mali, wadda aka kafa bayan juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin baya a watan Mayu ba ta ce komai ba a kan harin.

Jagoran juyin mulkin Mali Kanar Assimi Goïta wanda ya nada kansa shugaban rikon-kwarya

Bayanan hoto, Jagoran juyin mulkin Mali Kanar Assimi Goïta wanda ya nada kansa shugaban rikon-kwarya

An kai wannan harin ne kwana daya bayan da masu tayar da kayar baya suka kai hari kan wata tawaga ta Majalisar Dinkin Duniya a arewacin kasar, inda suka kashe farar hula daya suka kuma raunata daya.

Hare-haren masu ikirarin jihadi sun karu a Mali bayan juyin mulkin soji biyu a cikin wata goma sha shida, abin da ya taimaka wajen haifar da gwamnatin tarayya mai rauni, da kuma sanya Faransa mai dakaru 5,100 a kasar dakatar da ayyukan soji na hadin guiwa, da sojin Malin.

Mummunan halin tsaron da ake ciki a kasar ya sa kamar yadda rahotanni suka bayyana, hukumomin Malin karkata ga neman taimakon sojin haya na Wagner ta Rasha.

BBC hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN