Yadda macizai ke samun kafar shiga shaddar zamani su sari mutane a Najeriya


Saran maciji na da matukar haɗari kana wadanda ya sara kan buƙaci kulawa ta musamman da agajin gaggawa don su rayu, don haka lokacin da akan ɓata kafin ma a kai ga isa asibiti daga gida kan kasance da haɗarin gaske.


Yanzu haka yadda ake yawan samun macizai da kan shiga cikin ban dakunan da wuraren bahaya a gidajen jama'a a garuruwa da manyan birane a Najeriya, ya zama wani babban abin damuwa da fargaba a tsakanin al'umma.


Mafi tayar da hankalin shi ne yadda macizan kan samu hanya ta cikin bututun da ke hada matattarar ba-hayar da ke waje da kuma cikin masai ba zato ba tsammani.


Duk da cewa ba kasafai ake samun irin wanna matsala ta saran maciji a manyan birane ba, da yawanci aka fi danganta wa yankunan karkara, amma kuma yanzu haka ana samun faruwar haka jefi-jefi a biranen inda galibi ake amfani da masai irin na zamani.


Sai bango ya tsage...

Masana sun ce idan macizan sun samu kafar da ba a toshe ba ta nan ne su kan shiga don neman abinci da kuma samun mafaka da kuma wuri mai sanyi, inda ta hakan ne sukan samu shiga ta cikin bandukunan zamani.


Dakta Babagoni Woru babban daraktan Asibitin Koyarwa na Jami'ar jihar Yobe arewa maso gabashin Najeriya ya yi wa BBC karin bayani cewa, macizai za su iya bi ta bututun ne saboda neman abinci da kuma wuri mai sanyi.


"Macizai suna daga cikin nau'in halittu da ake kira "cold blooded" wato ba sa son zafi, jikinsu ba zai iya sarrafa yanayi ba kamar mu Æ´an adam, don haka a ko da yaushe suna neman wuri mai sanyi ne, musamman ma bandaki irin na zamani saboda ruwa da yake biyo bayan gida ta bututu yakan sa su ji sanyi yadda suke so," ya ce.


Dakta Goni ya kuma ce dole sai an kiyaye wajen kula da duk wata kafa ta waje inda ramin kankaren da ke tara ba-hayan da ke gagarowa daga bututun da yake hade da cikin bayan gidan.


"Da zarar sun samu wata kafa sukan shiga ta nan ne zuwa cikin bandakin saboda wurin ba ya rabo da sanyi," ya ƙara jaddadwa.


Masu aikin famfo da kuma hada masai na zamani sun sha bayyana yadda suke cin karo da irin wadannan halittu masu hadari a cikin gidaje, da suka hada da cikin rufin kwano da kuma ramukan bulo da ba a riga an yi wa yabe ba, ballantana kuma ramin kankare na matattarar ba hayar da ake kira soak away.


Malam Zayyanu daya daga cikin masu aikin famfo da gini ne a birnin Kano, kuma ya shaida wa BBC cewa rashin kula da ramin na soak away din ne yake sa macizan iya shiga har su kai da bulla ta hanyar bututun zuwa cikin bandakuna.


"Saboda shi ana so a kange shi ka da a bar wata kofa sai inda iska za ta rika fita, amma ita ma sai an saka rariya san saka.


"Saboda shi maciji ba ya raina rami, shi ba rami yake yi da kansa ba, don haka da ya samu kafa kawai sai ya wuce ta cikin bututun da ke hade da bandaki ya yi shigewarsa," in ji malam Zayyanu.


A duk lokacin da ake maganar cewa macizai na shiga cikin ta irin wannan hanya ta baya ya kuma shiga bandaki ta cikin masai, mutane da dama kan riƙa tunanin cewa ba abu ne mai yiwuwa ba ganin cewa a ko da yaushe akwai ruwa a cikin matsugunin.


Amma a cewar malam Zayyanu ruwa ba ya hana shi shiga cikin masan.


Ya kuma ce "Ai shi ruwan iyakacinsa cikin wannan kwamin da ke kasan masai din ne da kwance wanda yake hada warin ba haya dawowa ciki, kuma ba ya hana maciji shiga."


Fargaba da taka-tsan-tsan

A baya-bayan nan ne dai wani sharɓeɓen macijin ya yi sanadiyyar mutuwar wata jami'ar sojin sama Lance Corporal Bercy a Abuja, bayan da ya sare ta a lokacin da ta tsuguna a kan masan da ke bandakin gidanta da ke barikin sojojin.


An kuma riƙa jimami da yaɗa faifen bidiyon a shafukan sada zumunta tun daga ranar da lamarin ya abku wanda ya tayar da hankulan jama'a.


Hakan ya zaburar da jama'a da dama a shafukan sada zumuntar inda suka cigaba da yada faye-yayen bidiyon yadda macizan kan shiga cikin masai, tare da jan hankulan mutane kan yadda za su bi domin samun kariya.


A ranar 2 ga watan Janairun shekarar 2020 ma an samu abkuwar irin wannan abin al'ajabi a garin Kaduna, inda wata mai juna biyu wata takwas ta gamu da ajalinta, bayan da wani katon macijin ya sare ta lokacin da ta tsuguna a kan masan.


Magudanan dagwalon bahayan kan kasance wata matattara ko mabiyar kadangaru da É“eraye da kyankyasai ne wanda kan ja hankulan macizan su shiga don samun kalaci da kuma wuri mai sanyi.


Baya ga macizai akan samu kyakwasai da kadangaru da dangoginsu a ciki, ta inda nan ne su kan samu mafaka su shiga cikin bututun da ke matattarar bahayar da galibi suke a wajen gidajen, ta inda sukan haduwa da tukunyar bahayan da ke cikin gida, da zarar an samu wata kafa kenan.


Mutane da dama BBC ta tattauna da su sun bayyana cewa sun razana tare da shiga taitayinsu wajen sauya yanayin yadda suka amfani da masan na zamani.


Hajiya Fatima Haruna da ke garin Kano a arewacin Najeriya ta bayyana cewa tun daga wannan lokaci ta sauya tunani game da shiga bandakin.


"Gaskiya na tsorata sosai saboda ina amfani da irin wannan masai, don haka yanzu babu yadda za a yi in shiga bandaki ban duba ko haska ba, sai na leka na tabbata babu komai ciki sannan in kwara ruwa sannan in tsuguna," in ji ta.


Hajiya Aisha Abdu wacce ke zaune a Abuja babban birnin tarayyar Najeriyar cewa ta yi ba ta taɓa zaton macicji zai iya bi ta bututu ya shiga cikin masan ba, amma kuma tun lokacin da ta sake samun wannan labari ta fara taka-tsan-tsan,


"Tun daga bakin kofa idan zan shiga nake fara dube-dube sai na leka ciki kafin in zauna, amma duk da haka sai in rika jin kamar macijin zai fito," in ji Aisha.


Tsaftace muhalli

Alhaji Babagoni Bade shugaban karamar hukumar Fune a jihar Yobe arewa maso gabashin Najeriya, ya bayyana nasa ra'ayin game da daukar matakan kariya daga macizan da cewa tsaftace muhalli na taka muhimmiyar rawa.


"Mataki na farko shi ne mu kula da tsaftace muhalli, a rika nome ciyayi da ƙone su, sannan a rika yawan feshi a cikin masai da kuma wajen gida, hakan zai iya korar macizai," in ji shi.


Dakta Babagoni Woru shi ma ya dada yin ƙarin hasken game da daukar matakan, inda ya bayyana muhimmancin tabbas ciyayi maboyar macizai ne da kuma ɓeraye da ƙadangaru wadanda su kan su kan iya janyo macizai don samun abin kalaci.


Ya kuma kara da cewa "Idan aka tabbatar wuri na da yawan macizai sai a rika yin feshin maguguna da za su hana macizai rayuwa a wurin."


Rashin maguguna ko makarin dafin maciji

Wata babbar matsala da ake fuskanta it ace rashin magungunan kashe dafin macijin a kanana da manyan asibitocin Najeriyar.


Hakan na haddasa asarar rayukan wadanda macizan suka sara da tare da bata lokaci ba.


Jihar Gombe na da tarihin yawan da kuma saran macizai a garin Kaltungo inda ake tafka asarar rayukan jama'a.


Mataimakin gwamnan jihar ta Gombe Dakta Manaasa Daniel Jatau ya shaida wa BBC cewa lallai kan wannan matsala ta zama babban kaulbale a gare su saboda karanci ko kuma tsadar magugunan dafin macijin.


"Kwanan baya an kawo mana tallafin magugunan, duk wanda ya je da sarar maciji ana bashi kyauta to said ai abin takaici komai ya tsaya," in ji dakta Jatau.


"Abin ya yi muni saboda kudin maganin yanzu ya yi tsada sosai, daga naira dubu 20, dubu 30 har 40, matsala ce babba," ya ce.


Akwai bukatar gwamnatoci su dauki matakan tabbatar da cewa ko wane asibiti da cibiyoyin kiwon lafiya na ajiye magugunan dafin maczan a fadin kasar saboda shirin ko ta kwana, lamarin da ya sa wasu ke cewa gwamnatocin sun gaza taimakawa.


"Ba wai mun gaza bane, akwai kungiyoyin bayar da agaji da a baya suna kokarin taimakawa, amma matsalar ita ce dabi'ar mutane a irin kasashe masu tasowa sai ka ga an kawo tallafi amma sai ka rika gani ana fitar da su ana sayarwa a kasuwa," in ji dakta Jatau.


"Shi yasa ake karancin samun irin wananan tallafi a yanzu".


Wasu daga cikin matakan kariya

A cewar masana dai, dole a fahimci cewa babu wanda ke da wata garkuwar jiki daga cizon maciji, don haka kowa zai iya samun kan sa cikin wanan hadari.

BBC Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN