Wani mutum mai shekaru 80, Vito Cagani, ya daba wa matarsa, Kyrychok, wuka a a ranar Kirsimeti bayan ta yi alkawarin za su yi kwanciyar aure amma ba canja ra'ayinta, PM News ta ruwaito.
Mutumin ya sha maganin kara karfin maza a yayin da ya zauna yana jiran ta a gidansa da ke Fanano di Gradara a gabashin Italy.
Rashin amincewar da ta yi masa yasa ya fusata shi, inda ya yi zargin tana soyayya da mai gidanta awurin aiki. Ma'auratan sun shafe kimanin shekaru 20 suna tare.
Mutumin, bayan caka wa matarsa mai shekaru 61 wuka har sau hudu har ma a zuciyarta, ya bar ta kwance cikin jini a kasa yayin da shi kuma ya hau gado ya yi kwanciyarsa, Daily Mail ta ruwaito.
Kamr yadda rahotani suka bayyana, bayan gari ya waye, ya yi karin kumallo, sannan ya fita da karensa waje suka yi tattaki suka dawo gida tamkar ba abin da ya faru.
Sannan sai ya kira mai gidan matarsa na wurin aiki a wayar tarho ya fada masa cewa ba zai sake ganin Kyrychok ba.
Cangini ya fada wa mai gidan matarsa cewa:
Mutumin, wanda ke da wurin cin abinci ya kira yan sanda, sannan suka ziyarci gidan wacce abin da ya faru da ita. Jami'an sun tsinci gawar Kyrcychok a kasa da raunin wuka a kalla guda hudu, har a zuciya.
Nan take aka kama Cangini aka tsare shi, an kuma gano makamin da ake zargin an aikata kisar da shi a gidan.
A halin yanzu ana cigaba da bincike a kan lamarin.
Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari