Sojoji sun ceto 'yan sanda 20 da 'yan ISWAP da BH suka yi garkuwa dasu a Yobe


Hedkwatar tsaro ta sanar da cewa, an ceto 'yan sanda 20 da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai wa sashen 'yan sanda da ke Buni Yadi a garin Buni Yadi.

Mukaddashin daraktan harkokin yada labarai na rundunar Birgediya Janar Benard Onyeuko, yayin da yake yiwa manema labarai karin haske kan ayyukan soji da ke gudana a cikin makwanni biyun da suka gabata ya bayyana hakan.

Ya kuma ce sun fatattaki ‘yan ta’addan daga sansanoninsu yayin da wasu suka mika wuya, The Nation ta ruwaito.

A cewarsa, a cikin lokacin da ake magana, an kashe jimillar ‘yan ta’adda 62 tare da kama 28.

Punch ta ruwaito shi yana cewa:

“A dunkule, an kashe ‘yan ta’adda 62, sannan an kama 28 daga cikinsu, sannan an kwato makamai iri-iri 54 da alburusai 144 daban-daban.

"Haka kuma, an kwato jimillar dabbobi 101 da aka sace, da kuma jami’an NPF 20, wadanda aka yi garkuwa da su a lokacin da ‘yan ta’addan suka kai hari a ofishin ‘yan sanda, sojoji Buni Yadi sun kubutar da su a cikin wannan lokaci.”

An kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a maboyar su da ke kusa da unguwar Ossra-Irekpeni da ke kan titin Okene zuwa Lokoja zuwa Abuja.

Daya daga cikin mafarautan yankin da suka kai harin ya shaida wa Daily Trust cewa an yi musayar wuta dasu.

Ya ce mafarautan tare da shugaban karamar hukumar Adavi ta jihar Kogi, Joseph Samuel Omuya, sun kai farmaki dajin ne bisa samun rahoton kasancewar 'yan ta'addan a yammacin Laraba.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN