Type Here to Get Search Results !

Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Kisa Saboda Kashe Kawunsa A Hadejia


Wata Babban Kotun Jihar Jigawa wanda take zaman ta a nan Hadejia a jiya ta yankewa wani Mai suna Magaji Husseini Lushe, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samun sa da laifin kashe kawunsa.


Da yake yanke hukunci Alkalin Kotun Mai Shari’a Ado Yusuf Birnin Kudu, ya ce Kotun ta samu mutumin wanda mazaunin Rigar Dadi Lamido dake Karamar hukumar Kirikasamma ne da laifin kashe kawun sa Muhammad Alhaji Amadu da wuka.


Alkalin Kotun ya ce mutumin da ake zargin ya amsa laifinsa, a lokacin da ya bayyana a gaban Kotun, inda ya ce aikata kisan.

SawabaFM

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies