Da mulkin farar hular nan, gara gwamnatin Sojoji inji Ministan Obasanjo da ya baro ta

Tsohon babban Ministan shari’a na kasa, Kanu Godwin Agabi ya yi kaca-kaca da tsarin da Najeriya take tafiya a kai da sunan mulkin farar hula. 

Jaridar This Day ta rahoto Kanu Godwin Agabi SAN yana cewa tsarin damukaradiyyan da kasar nan ta ke aiki da shi ya ba shugaban kasa karfi da yawa. 

Tsohon lauyan na gwamnatin tarayyar ya bayyana haka ne da yake bayani a wajen wata lacca da aka shirya domin tunawa da Mai shari'a Ambros Allagoa. 

Rahoton yace Marigayi mai shari’a, Ambros Allagoa shi ne mutumin Najeriya na farko da ya rike kujerar babban Alkalin Alkalai a tarihin tsohuwar jihar Ribas. 

An tuna da Ambros Allagoa Da yake bayani a wajen taron a garin Yenagoa, jihar Bayelsa, Agabi yace mulkin sojoji ake yi da sunan farar hula, yace an fake ne kurum da tsarin mulki 

Allah wadaran wannan siyasa 

“Tsarin gwamnatin da ake yi kama-karya ne kurum aka fake da tsarin mulki, saboda an tattara karfin an ba mutum daya; shugaban kasa ne ko gwamna.” 

“Mun zabi wannan tsari saboda akwai yiwuwar samun rabuwar kai a kasa, da sa ran cewa idan iko ya fada kan mutum daya, za a gina kasa.” – Agabi SAN. 

Babban Lauyan ya kara da cewa siyasar da ake yi a kasar nan ita ce a kassara ‘yan adawa. 

Kanu Godwin Agabi ya soki tsarin mulkin da ake amfani da shi, yace bai da maraba da mulkin soja

Babban lauyan ya bayyana wannan ne a wajen wata lacca da ya gabatar a Garin Yenagoa, Bayelsa Agabi SAN yace ana amfani da kundin tsarin mulki ana gwamnatin kama-karya a harkar siyasa 

Kanu Godwin Agabi ya yi kaca-kaca da tsarin da Najeriya take tafiya a kai da sunan mulkin farar hula. 

Jaridar This Day ta rahoto Kanu Godwin Agabi SAN yana cewa tsarin damukaradiyyan da kasar nan ta ke aiki da shi ya ba shugaban kasa karfi da yawa. 

Tsohon lauyan na gwamnatin tarayyar ya bayyana haka ne da yake bayani a wajen wata lacca da aka shirya domin tunawa da Mai shari'a Ambros Allagoa. 

Sanata Kalu ya bayyana darussan da ya koya Rahoton yace Marigayi mai shari’a, Ambros Allagoa shi ne mutumin Najeriya na farko da ya rike kujerar babban Alkalin Alkalai a tarihin tsohuwar jihar Ribas. 

An tuna da Ambros Allagoa Da yake bayani a wajen taron a garin Yenagoa, jihar Bayelsa, Agabi yace mulkin sojoji ake yi da sunan farar hula, yace an fake ne kurum da tsarin mulki. 

“Tsarin gwamnatin da ake yi kama-karya ne kurum aka fake da tsarin mulki, saboda an tattara karfin an ba mutum daya; shugaban kasa ne ko gwamna.” 

“Mun zabi wannan tsari saboda akwai yiwuwar samun rabuwar kai a kasa, da sa ran cewa idan iko ya fada kan mutum daya, za a gina kasa.” – Agabi SAN. 

Babban Lauyan ya kara da cewa siyasar da ake yi a kasar nan ita ce a kassara ‘yan adawa.  akwai yiwuwar a sake rufe jami’o’i gwamnati a Najeriya 

A wajen wannan lacca, Agabi ya ce dole gwamnatoci a kowane mataki su fahimci cewa adawa mai ma’ana ta na da amfani domin a bunkasa siyasar kasar.

 “Muddin aka kashe adawa ko ba ta aiki, gwamnati ba za tayi aiki da kyau ba, kuma idan aka samu wannan, bangaren shari’a ba zai yi aiki da kyau ba.” 

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN