Akalla mutum biyu sun rasa rayukansu yayinda akayi awon gaba da mutane 50 yayinda yan bindiga suka kai hari Unguwar Gimbiya dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Wani mai idon shaida wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa manema labarai cewa wannan hari ya auku ne sa sanyin safiyar Juma'a, 3 ga Disamba, 2021.
A cewarsa an bindigan sun kai gari gidaje akalla 13 kuma sai da suka kwashe sa'o'in biyu suna diban jama'a.
Yace: "Sun kai garmaki Ungwan Gimbiya dake Sabo, karamar hukumar Chikun dake Kaduna, sun kashe mutum 2, sun sace 50."
Wani mazaunin daban, Gideon Jatau, a cewar Daily Trust, yace ba'a taba kai hari irin wannan ba a garin. Yace suna fuskantar lamari sace-sacen mutane amma wannan ya yi munin gaske.
Yunkurin samu karin bayanai daga bakin Kakakin yan sandan Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya ci tura.
Source: Legit.ng News
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI