Da duminsa: Wani mutum ya mutu garin satar wayar transfoma, duba yadda ta faru


Wani mutum ya rasa ransa yayin kokarin satar wayoyin transifoma da sanyin safiyar Alhamis a Labour Quarters da ke garin Tunfure a karamar hukumar Akko cikin jihar Gombe, The Nation ta ruwaito. 

Dr Adakole Elijah, shugaban bangaren yada labarai na kamfanin rarraba wutar lantarki na Jos (JEDC) ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilin NAN a Gombe ranar Alhamis, Vanguard ta ruwaito. 

Elijah ya ce: “A ranar 16 ga watan Disamba da misalin karfe 3:30 na asuba, wani barawo ya rasu yayin da ya ke satar wayoyin transifoma din Labour 1 da ke Tumfure. “Mutumin ya so sace wayar kebur din da ke saman transiforma din ne.” 

Yan sanda aka kai wa rahoton mutuwar mutumin A cewarsa an kai wa ofishin ‘yan sanda da ke Tumfure rahoto daga nan ‘yan sandan su ka dauko gawarsa wanda har yanzu ba a gane ko wanene shi ba. 

Ya bukaci mazauna yankuna da su kasance masu kula sannan su dinga kai rahoto akan duk wani lamarin sata, yayin da ya ja kunnen masu barna akan kiyaye yin hakan saboda hatsarin da ke gabansu. 

Elijah ya ce JEDC ta fara sa fitillu masu amfani da hasken rana kusa da transfomomi don haske ya hana masu barna aiwatar da hakan. 

Wani mazaunin yankin ya ce wayoyin wuta barayi ke sacewa Wani mazaunin yankin, Zakari John ya sanar da NAN cewa wannan ba shi ne karo na farko ba da irin hakan ya faru, kuma faruwar hakan na janyo a dakatar da kai wuta a anguwanni. 

John ya bayyana yadda su ka taba yin kwana biyar lokacin da aka lalata transformer din anguwarsu wanda ya ja sai da su ka hada kudi kafin su gyara. 

“Wayoyi dama su ke sata,” a cewarsa. Ya roki JEDC akan samar da fitillu masu amfani da rana kusa da transformomi don mutanen anguwanni su dinga lura da abubuwan da ke aukuwa kusa da su. 

Legit Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN