An gano gawarwakin mutane a yashe, wasu a bushe, sa'ilin da wasu daga cikinsu an gasa su


Jami'an rudunar tsaro ta farin kaya, ta DSS ta gano wasu sansanoni da ake kashe tare da gasa gawarwakin mutane domin ci a cikin jihohin Imo da Anambra.

An ga kawunan mutane a yanke kuma a warwatse a sansanonin masu garkuwa da mutane a jihar.

Tuni dai hukumar ta kama wasu wadanda ake zargi da hannu cikin miyagun ayyuka da ba su yi kama da na bil adama ba.

Tawagar jami'an tsaro ta hadin gwiwa ce ta kai samamen ba zata a sansanonin masu garkuwa da mutane a jihohin Imo da Anambra; inda suka riske gawarwakin mutane a yashe, wasu a bushe a sa'ilin da wasu daga cikinsu kuwa an gasa su wanda ake zargin mutanen da ke garkuwa da bil'adaman kan ci.

Wannan yunƙuri dai ya kai ga kama masu garkuwa da mutane sama da 30 a waɗannan sansanoni.

Daraktan hukumar DSS a jihar Imo, Wilcox Idaminabo, ya ce: "Rundunar tsaro ce ta hadin gwiwa da ta hada da sojoji, 'yan sanda da kuma DSS suka gudanar da wannan aiki.

"Mun kai farmaki ga maboyar masu garkuwa da mutane a wata unguwa a jihar Anambra da kuma Orsu a jihar Imo.

"Al'umma sun yi gudun hijira, babu wanda ke zaune a wurin. Yaran sun mallakarwa kansu wani sansani mai yawa kuma wannan wani lamari na tayar da ƙayar baya ne. Babu wanda ke zaune a wurin.

"A yayin da ake gudanar da wannan samamen ne, jami'an tsaro suka samu nasarar ceto Eze Acho.

Wannan samamen da jami'an hadin gwiwa suka gudanar a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo da kuma Uli da ke karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra, ya yi sanadin kama mutum sama da30 da ake zargi sun mayar da sassan jikin bil'adama abincinsu.

Kuma a wurin ne jami'an suka kubutar da Eze Acho Ndukwe na al'ummar Ihube a karamar hukumar Okigwe ta jihar Imo, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar Lahadi.

Mista Idaminabo ya ƙara da cewa: "Kuma mun gano gawarwaki da dama da aka daddatsa da yanke kawunansu.

"Ina mamakin, a cikin karni na 21, mun lura cewa har yanzu mutane suna cin naman mutane a nan. Mun ga naman mutum a gashe.

"Mun ga gawarwaki da yawa. Abin da suke yi shi ne garkuwa da kashe wasu daga cikin mutanen.

"Hakika, sun yi musayar wuta da jami'an tsaro, amma mun rinjaye su kuma muka kama da yawa daga cikinsu," kamar yadda ya ce.

Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma ya ce gaskiya ta yi halinta cewa wadanda ke aikata miyagun ayyuka kamar waÉ—annan su ne annobar wannan yankin Igbo a kudu maso gabashin Najeriya.

Ina so in yaba wa jami'an tsaro a jihar Imo da suka hada kawunansu tare da tabbatar da cewa akalla mutanen Imo sun dawo gida su yi bukukuwan Kirsimati.

Lamari ne na matukar nuna damuwa da mamakin yadda daukacin karamar hukuma kamar ta Orsu za a yi watsi da ita har ta fada a hannun masu masu cin naman mutane. Daga abin da muka gani yanzu za ku yarda da ni cewa wadannan miyagun mutane ne da basu da wata makoma ta alheri da suke shirya-wa kansu. Ta ya zasu gasa kuma su ci naman bil'adama in ba dabbobi masu cin naman mutane ba?

Ta yaya kuma za mu bi da irin wadannan wawaye idan ba doka ta yi aikinta ba ba?

Cin naman mutane har yanzu a wasu kasashen duniya na a wannan zamani, duk da cewa galibin al'ummomi suna ɗaukarsa abin ƙyama.

Duk da haka, akwai wuraren da cin naman É—an adam ya kasance tamkar wani bangare na al'ada.

Mutane suna komawa cin naman mutane saboda wasu dalilai, kama daga bukukuwan addini zuwa matsananciyar bukata ta abin duniya da dai sauransu.

Rahotun BBC Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN