Gwamna Duoye Diri na jihar Bayelsa ya rantsar da matarsa, Patience Zuofa-Diri, da wasu masana shari'ar uku a matsayin alkalan babba kotun jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Baya ga matar Diri, sauran sabbin alkalan sun hada da tsohon magatakardan babbar kotun jihar Bayelsa, James Lookie, lakcara a fannin shari'a na jami'ar Niger Delta, Dr. Simon Amaduobogha da kuma lauya Christine Enegesi
A yayin basu rantsuwar kama aiki a matsayinsu na sabbin alkalai a gidan gwamnatin jihar da ke Yenagoa, Diri ya ce mulkinsa ya na bai wa fannin shari'a fifiko ganin irin rawar da suke takawa a al'umma.
Ya kara da tuna abun kunya irin kutsen da aka yi a gidan alkalin kotun koli, Mai shari'a Mary Odili, inda yayi kira ga hukummin da suka dace da su dauka mataki kan masu hannu a ciki.
Gwamnan ya taya sabbin alkalan murna kan sabon mukaminsu da cigaban da suka samu, inda yayi kira garesu da su buata wa mutane yadda ya dace, Daily Trust ta ruwaito.
Ya jinjinawa NJC, hukumar shari;a ta jihar, babban alkalin jihar da kuma alkalin alkalan Najeriya kan yadda suka amince da zabin babu bata lokaci.
Ya ce an gano cewa sun dace da wannan ofishin bayan sun cika wasu manyan sharudda.
Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/G83TOEf1MUmDTiYaMTb02g
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI