A halin yanzu, shugaban 'yan bindigan Zamfara da Sokoto, Bello Turji, ya nakasa sakamakon miyagun raunikan da ya samu a samamen da soji suka kai maboyarsa Ba a nan sojojin Najeriyan suka tsaya ba, sun kai samame sansanonin 'yan bindiga da ke garuruwan Isam Sabon birni da gabashin Tozei Wasu daga cikin 'yan bindigan sun tsere da miyagun raunika tare da basu wasu makamansu amma sojin kasa sun bii su tare da mitsike su
Wata majiyar sirri ta sojojin Najeriya ta sanar da PRNigeria cewa, luguden ruwan wutan ta sama wanda aka hada da luguden sojin kasa, an yi shi ne a garin Shinkafi na jihar Zamfara da kuma Bafarawa da ke garin Sabon Birni a jihar Sokoto.
Kamar yadda majiyar sirrin ta bayyana, har yanzu ba a san yawan 'yan bindigan da aka sheke ba a samamen asubahin da suka kai.
PRNigeria ta tattaro cewa, wasu daga cikin 'yan bindigan da suka samu miyagun raunika sun yi kokarin tserewa amma sojin kasa sun yi musu kwanton bauna.
"Bayan ayyukan kawar da 'yan ta'addan da aka yi a jihohin Katsina da Zamfara daga ranakun 16-17 ga watan Disamba, sojin sun yi lugude da jiragen yaki a sansanonin 'yan bindiga da ke Sabon Birni, Isa da gabashin Tozei inda aka kashe 'yan bindiga masu yawa yayin da wasu suka tsere.
Har ila yau, a safiyar 18 ga watan Disamba, sojin saman sun yi luguden wuta a kauyen Gebe da ke jihar Sokoto inda 'yan bindigan ke ta hantarar mutane amma sojin suka ragargajesu.
"A wurin, 'yan bindiga marasa yawa ne suka tsere inda suka bar makamansu," majiyar tace
Legit Hausa
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari