Mazaunan rukunin gidajen 1000 Housing Estate dake cikin Maiduguri sun waye gari ranar Asabar da tashin bama-bamai.
Vanguard ta ruwaito cewa akalla karar bama-bamai hudu aka ji cikin gundumar Gomari da 1000 Housing Estate.
Ana kyautata zaton cewa yan ta'addan Boko Haram suka kai wannan hari ta hanyar harba rokoki cikin gari yayinda Sojoji ke kokarin kawar da su. A cewar wani mai idon shaida, bama-bamai biyu sun fara tashi ne a tashar jirgin sama dake Gomari.
Na godewa Allah, mutumin da ya tsallake rijiya da baya Wani mutumi da ya tsallake rijiya da baya bayan roka ya dira cikin gidansa, Mallam Kulima, ya mika godiyarsa ga Allah bisa kare rayuwarsa da na iyalansa.
Yace: "Yau ranar bakin ciki ce a 1000 Housing Estate, Borno, saboda Roka ta dira cikin gidana dake 2589, Elkenemi street." "Ina cikin daki lokacin da rokar ta dira dakin uwargidata."
"Wasu daga cikin iyalina sun samu raunuka iri-rir kuma an garzaya da su asibiti." Wani mazauni mai suna Usman Ali yace: "Tashin bam din ya lalata wani gida dake kusa da gidana, bai kashe kowa ba amma wani karamin karamin yaro dan shekara 9 ya ji rauni."
Wani mai idon shaida, Usman Zanna Gomari yace: "Muna zargin yan Boko Haram ne suka harba kuma muna tunanin suna son kai hari masaukin maniyyata aikin Hajji (Hajj Camp) inda aka ajiye tubabbun yan Boko Haram."
"Ka san mun dade muna korafi kan cigaba da ajiye tubabbun yan ta'addan cikin gari. Idan ka lura, sun dade suna kai hare-haren unguwannin da aka ajiye tsaffin abokansu."
Source: Legit Newspaper
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI