Da duminsa: Cutar Korona ta barke a fadar shugaba Buhari, duba manyan hadimai da suka kamu...


Sabuwar nauyin cutar Korona ta barke a fadar Shugaban kasa, Aso VIlla, inda manyan hadiman Shugaba Buhari da manyan jami'an gwamnati suka kamu da cutar. 

Premium Times ta bankado cewa sakamakon gwajin da aka gudanar ya nuna cewa akalla manyan na kusa da Buhari guda hudu sun kamu da cutar. 

Daga cikinsu akwai Sakataren din-din-din na fadar Shugaban kasa, Tijjani Umar; Dogarin Buhari, ADC Kanal Yusuf Dodo; CSO Aliyu Musa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu. 

Hakazalika akwai Ministan Labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, shima sakamako ya nuna Korona ta hau shi. 

Rahoton ya kara da cewa a ranar Laraba, an yakice Garba Shehu da wasu daga taron majalisar zartaswa ranar Laraba yayinda sakamakon gwajin PCR ya fito. 

Garba Shehu ya tabbatar da cewa lallai ya kamu da cutar a sakon da Premium Times tace ta gani. 

Yace: "Ban da tabbacin wadannan mutanen da ka ambata amma na kamu da sabon nauyin cutar maras tsanani. Tun farko ban ji komai ba, la'alla saboda na yi rigakafi sau uku ne, amma yanzu garau nake ji."

 "Amma matsalar cutar nan itace sai abinda masana kimiya suka fada cewa kaji sauki. Yanzu dai ina killace kuma zan koma in sake gwaji don ganin ko har yanzu akwai cutar ko ta tafi." 

Duk yunkurin yi daga bakin Lai Mohammed, Femi Adesina, Tolu Ogunlesi, ya ci tura. 

Amma majiyoyi masu karfi sun bayyana cewa dukkan jami'an da suka kamu na killace kuma ana kula da su. 

Source: Legit.ng 

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN