Shugabannin ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gabatar da sunan Muazu Sambo, a matsayin sabon ministan da zai naɗa daga jihar Taraba ga majalisar dattijai.
Dailytrust ta ruwaito cewa Sambo zai maye gurbin tsohon ministan samar da lantarki, Sale Mamman, wanda shugaban ya sallama daga aiki tare da tsohon ministan noma, Sabo Nanono a watan Satumba da ya gabata.
Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, shine ya karanta wasikar neman amincewa da shugaba Buhari ya aike wa majalisar a zamanta na yau Talata.
Buhari ya naɗa kwamishinonin INEC Haka nan kuma, shugaba Buhari ya bukaci majalisar ta tantance sabbin kwamishinonin zaɓe na ƙasa da kwamishinan zaɓe jiha guda ɗaya na INEC.
Waɗan da shugaban ya nemi majalisa ta amince da sun haɗa da; kwamishinonin zaɓe, Malam Mohammed Haruna (Niger), May Agbamuche Mbu (Delta), Okeagu Kenneth Nnamdi (Abia) da Manjo Janar A.B. Alkali (mai ritaya.) (Adamawa).
Sauran sun haɗa da; Farfesa Rada H. Gumus (Bayelsa), Sam Olumeko (Ondo) duƙ a matsayin kwamishinonin INEC na ƙasa, sai kuma Olaniyi Olaleye Ijalaye (Ondo) a matsayin REC.
Wasu daga cikin kwamishinonin hukumar zabe INEC sun yi aiki tare da shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, a zangon mulkinsa na farko, wanda daga baya Buhari ya sake naÉ—a shi a karo na biyu.
Buhari ya naɗa kwamishinonin NPC Kazalika shugaban ƙasa Buhari ya nemi amincewar majalisar dattawan wajen naɗa kwamishinonin hukumar kidaya ta ƙasa (NPC).
WaÉ—an shugaban ya aike da sunayen sun haÉ—a da; Injiniya Benedict Opong (Akwa Ibom), Gloria Izofor Mni, Barista Patricia O. Iyayan Kuchi (Benue), Dakta Bala Haliru (Kebbi) da kuma Dakta Iyatayo Oyetunbi (Oyo). A wani labarin kuma
Source: Legit
Reported by ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg
Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN
Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN
Shafukan sada zumunta
Twitter twitter.com/isyakalabari
Facebook facebook.com/isyakalabari
Rubuta ra ayin ka