Birnin kebbi: Yaron da aka daure a turakun dabbobi a Badariya ya samu lafiya Gwamnati ta mayar da shi ga iyayensa (Hotuna)Gwamnatin jihar Kebbi ta mayar da Jibril Aliyu ga iyayensa. Jibril shi ne yaron da kishiyoyin mahaifiyarsa suka daure a turakun dabbobi a Unguwar Badariya a garin Birnin kebbi shekara daya da ta wuce. Shafin isyaku.com ya wallafa.

Gwamnatin jihar Kebbi ta dauki nauyin jinyar Jibrin har zuwa wannan lokaci. 

Kazalika mun samo cewa akalla Likitoci 20 sun duba lafiyar Jibrin a tsawon lokacin da yake karkashin kulawar Gwamnati dangane da harkar lafiyarsa.

Sai dai babban Kotun Majistare da ta yi zamanta a Birnin Kebbi ranar 29 ga watan 7, 2021, karkashin Mai sharia Mungadi, ta daure Mahaifin Jibrin mai suna Aliyu Umar tsawon shekara daya a Kurkuku karkashin doka ta 238 na Penal code ba tare da zabin biyan tara ba sakamakon kama shi da laifin cin zarafin yaron.

Yanzu haka yaron ya murmure kuma an mayar da shi wajen iyayensa.

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN