An kuma: Kwankwaso ya sake baro babbar magana, ya ce ....


Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya nuna damuwa kan yadda sha'anin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a Najeriya musamman a arewacin kasar.

Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da BBC Hausa.

Sanata Kwankwaso yana gani barin matsalar da aka yi ta dauki lokaci ba tare da daukar mataki ba shi ya sa yanzu take neman gagarar hukumomi.

Ya kara da cewa abubuwan da ke faruwa a Najeriya suna da ban mamaki, yana mai cewa daga lokacin da ya bar ma'aikatar tsaro a matsayin minista kawo yanzu bai taba zaton matsalar za ta tabarbare haka ba.

"Batun da ake yi ba na shugaban kasa ba ne, batu ne da mun san shugaban kasa sai an gama komai ake fada masa amma yanzu lamarin ya sauya," in ji shi.

Ya ce: "Abubuwan da suka janyo matsalar nan kashi-kashi ne: na farko akwai kura-kurai da shugaban kasa ya aikata da suka dagula lissafi, saboda a matsayin da shugaban yake ya kamata ya yi tafiya da kowa da wadanda suka taimake shi da wanda bai taimaka maka ba. Sannan a matsayin shugaba da zarar an rantsar da kai bai kamata a ce wane ba ka son sa ba, ko wane ba shi da amfani ba."

Kwankwaso ya ce ya kamata 'yan Najeriya su hada hannu wajen taimaka wa shugaban kasa da jami'an tsaron domin yin shawo kan matsalar. "A hadu a duba me ya kamata a yi domin shawo kan matsalar."

Da aka tambayi Kwankwaso ko yaya yake ganin rawar jami'an tsaron Najeriya sai ya ce "babban abin mamaki sai ka ji an ce an kashe mutum kaza, amma ba za ka ji an yi komai ba. Kuma kullum mutanen nan [ 'yan bindiga] kara samun kudi da kayan aiki da nasara suke yi, har a wasu wuraren muna jin ana cewa suna karbar haraji.

A kasa kamar Najeriya, da soja na sama da na kasa, a ce an kai matsayin a shekarar 2021 wadanda su mutane da yawancinsu ba su da ilimin Arabiya babu na zamani, a ce sun yi karfin da suka ware wani sashe na Najeriya kuma an yi shiru an zura musu ido ba tare da daukar wani mataki ba, wai shin me ya ke faruwa ne?," in ji Kwankwaso.

Gwamnatin Najeriya dai ta sha nanata cewa har yanzu akwai matsala a arewa maso gabashin kasar, can kudu ma akwai matsalar 'yan aware maso son kafa jamhuriyar Biafra wato IPOB, ga kuma abin da ke faruwa a arewa maso yammacin kasar, hakan ya sa wasu ke ganin ne ya yi wa jami'an tsaro yawa don haka ake ganin gazawarsu.

Sai dai Kwankwaso na da ra'ayin cewa ba haka lamarin ya ke ba, da an dauki mataki akan barayin daje da ke jihar Sakkwato, aka yi ta yadda kowa zai gani da tuni wasu da ke son aikata hakan sun sauya tunani, ya boye bindigarsa ya gudu. ''Amma abin damuwa da tashin hankalin shi ne har suna ake radawa iin wadannan barayi, wanda ya yi kaurin suna anan arewa wai sunansa Babban sufeton 'yan sanda,'' in ji Kwankwaso

Rahotun BBC Hausa

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga Group dinmu na Whatsapp domin samun labaranmu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/CTugsexjJhBCwuOLVzkGrg

Domin aiko labari mu wallafa maka LATSA NAN

Domin zama Wakilinmu a garinku LATSA NAN 

Domin Korafi/Tuntubemu LATSA NAN

Shafukan sada zumunta

Twitter twitter.com/isyakalabari

Facebook facebook.com/isyakalabari

 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN