'Yana da katon al'aura da ya fi karfina" Amarya ta roki Kotun Shariar Musulunci ta raba aurenta da Angonta mako daya bayan daura aure a Gusau


Wata Amarya mai suna Aisha Dannupuwa, ta roki Kotun Shariar Musulunci da ke unguwar Samaru a birnin Gusau ta kashe aurenta da angonta saboda gazawarta wajen jure kwanciyar aure tare da angonta. Shafin isyaku.com ya samo.

Dailypost ta labarta cewa Aisha Dannupuwa ta gaya wa Kotu cewa saduwarta na aure tare da angonta bala'i ne a gareta saboda al'aurarsa ya yi mata girma kwarai.

Ta ce:

"Lokacin da muka yi kwanciyar jima'i da shi na sha wuya saboda girman al'aurarsa. Marmakin in ji dadi tsananin ukuba na sha saboda al'aurarsa ya yi mani girma".

" Bayan kwana biyu ya sake dawowa kuma muka yi kwanciyar jima'i da shi. Sai dai ko a wannan karo na sha tsananin wuya da azaba saboda girman al'aurarsa ya fi karfi na. A nan ne na fahimci cewa ni ba zan iya ci gaba da wannan aure ba saboda al'aurarsa ya fi karfina". Ta Kara gaya wa Kotu.

Shi dai angonta ya amince da bukatarta. Ya kuma yarda Kotu ta raba aurensu da aka daura tsawon mako daya kacal.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN