Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: An ceto Jariri dan kwana daya da haihuwa da mahaifiyarsa wata Bazawara ta jefar a cikin rijiya a jihar Jigawa, duba abin da ya faru


An tsinci wani Jariri Dan kwana daya da aka yar a cikin wani rijiya a kauyen Garin Ganau da ke karamar hukumar Babura a jihar Jigawa. Shafin isyaku.com ya samo.

Wasu manoma da ke wucewa ta gefen rijiyar suka jiyo kukan jaririn a cikin rijiyar lokacin da suke wucewa zuwa gona ranar Juma'a 26 ga watan Nuwamba.

An yi nassarar ciro jaririn a cikin rijiyar.

Shafin isyaku.com ya ruwaito cewa Kakakin hukumar yansandan jihar Jigawa ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar wa Daily Post da faruwar lamarin. 

Ya ce bayan an ciro jaririn daga cikin rijiyar, an kai shi babban Asibitin garin Babura inda aka duba lafiyarsa, daga bisani aka sallame shi. An mika jaririn ga sashen kula da jin dadi da walwalar jama'a na karamar hukumar Babura.

Ya ce sakamakon haka Yan sanda suka shiga bincike da ya kai su ga kama mahaifiyar jaririn, wata Bazawara yar shekara 35 mai suna Ni'ima Yakubu, kuma ana ci gaba da bincike. Inji ASP Lawal. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies