Yadda buga cacar wasanni ke mamaye zukatan yan Najeriya da cinye tattalin arzikinsu


Duba da yanayin tattalin arzikin da muke ciki, zuba kudi a harkar cacar wasanni a yanzu ya zama ruwan dare musamman ga mabiya manyan addinai biyu, Musulunci da Kiristanci.

Dailytrust ta tattaro cewa cacar wasanni a halin yanzun ya zama kasuwanci mafi sauki ga yan Najeriya.

Matasa da kuma manyan mutane daga kowane ɓangare sun jefa kansu cikin cacar wasanni yayin da kowane ke fatan zama zakara a ƙarshe.

Kowace caca, karshenta na zamo wa farin ciki ga wasu, yayin da wasu kuma ke shiga halin takaici da bakin ciki.

A shekaru da dama da suka wuce, masu buga caca suna zuwa shagunan da ake kira "Pool" da takardun shaida domin buga cacarsu.

Amma a halin yanzun, bisa samun cigaban fasaha ta kirkirar yanar gizo, kamfanonin caca sun samu cigaba da dama.

Adadi mai yawa na masu buga caca na da damar yin harkokinsu daga dakin kwanan su saboda cigaban da aka samu, wanda yasa kamfanonin caca suƙa ƙaru a Najeriya.

Kamfanonin caca a Najeriya

A ranar 7 ga watan Satumba, 2018, Hukumar kula da harkokin caca a Najeriya, (NLRC), ta bada lasisin gudanar da kasuwanci na farko ga kamfanin caca na AfriBet.

Zuwa yanzun akwai kamfanonin caca sama da 36 da suka samu lasisin kasuwanci a Najeriya.

Daga cikik irin waɗan nan kamfanonin akwai, Bet9ja, Betway, Nairabet, Naijabet, Betwinner, Betbigi, Cloud Bet, Sportybet, iBet, Access Bet, BetLion, Melbet, MerryBet, BetKing da ZeBet.

Waɗan nan kamfanoni na samun makudan kudi daga hannun yan Najeriya kuma sun faɗaɗa harkokin su zuwa kowane lungu da sako na kasar nan.

Da wahala a samu wani sashi na Najeriya da caca ba ta shiga ba, duk da rashin ingancin wutar lantarki, domin za'a iya buga caca a kan intanet da kuma a shaguna.

Duk da amfani da kamfaninin caca ke wa tattalin arzikin kasa, amma lamarin ya zama wata takobi mai kaifi biyu. Mutane da caca ta zama musu jiki, asarar da suke yi ta zarce ribar da suka samu a tsawoɓ shekarun da suka shafe.

Yadda caca ta shiga jinin mutane

A zahirin gaskiya, mutane da dama zasu ce caca ta zama jinin yan Najeriya, domin zai yi wahala mai buga caca ya iya faɗa maka lokacin da zai bari.

Wani mazaunin jihar Legas, Abbey, ya tsunduma cikin harƙar caca a wasanni, yace yana zuba kudi a harkar caca akai-akai amma har yanzun bai taɓa amfani ba dun da mukadan kudin da yake zuba wa.

Yace:

"Na zuba kudi da yawa a caca, kuma ina samun nasara. Amma kudin da na samu ba su taka kara ba idan na kwatanta da waɗan da na kashe a ciki."

"A koda yaushe na samu kudi sai inji ina son buga wasan caca, akwai waɓda ake buga wa da safe, akwai na dare da kuma na yamma.Na kan shiga da zaran na samu kudi."

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN