Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: Yansanda sun bindige kasurgumin dan bindiga Yellow Magaji da yake addabar matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja (Hotuna)


Yansanda sun bindige kasurgumin dan bindigannan Yellow Magaji da ya dade yana addaban hanyar Kaduna zuwa Abuja. Shafin isyaku.com ya samo.

Kakakin hukumar yansandan jihar Kaduna ASP Muhammed Jalige ne ya sanar wa manema labarai ranar 27 ga watan Nuwamba.

Ya ce yansanda tare da hadin gwiwa da sashen FIB na yansanda sun kai wani samame a wani Otel da ake kira SIR JOE GUEST INN da ke lamba NO.8 Sajo Street, Unguwan Maigero a Sabon Tasha da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna,.inda yan bindigan suka kama daki.

Yan bindigan sun bude wa yansanda wuta  da bindiga lokacin da suka farga cewa yansanda suna kokarin kama su. Sun yi ta buda wuta suna harbe harbe sakamakon haka yan sanda suka mayar da martani da harbin bindiga.

Lamari da ya kai ga yi wa Yellow Magaji a.k.a Arushe mumunan rauni. yayin da abokinsa, Yellow Ashana tare da sauran yan bindigan suka tsere da raunukan harsashi. 

Daga bisani Yello Magaji ya mutu bayan yansanda sun kai shi asibiti domin a ceto ransa, amma Likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Yan sanda sun kama bindiga kirar AK47 guda daya tare da babur kirar BOXER. Kazalika yansanda sun kama Manajan Otel inda yan bindigan suka kama daki domin a yi masa tambayoyi.

 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Hollywood Movies