Ya kwace mana matanmu na aure, Mazajen sun kai karar wani Fasto


Tashar Human Right Radio wacce aka fi sani da Brekete Family dake Abuja ta daura hotunan wasu mazaje da suka kai karar wani Fasto Harrison Anazodo Charles kan laifin kwace musu mata, da 'yayansu. 

A cewar Brekete Family, mazajen sun zargi Faston da sihirce musu mata. Daya daga cikinsu yace: "Iyalina ta dawo daga Coci ta sanar da ni cewa Fasto ya fada mata daga yanzu aurenta da mijinta ya mutu." 

Ta fita daga gidan Ya kara da cewa lokacin da ta fada masa haka, ya dauka wasa take yi. Amma daga baya ta kwashe kayanta gaba daya daga gidan. 

Nima ya kwashe min mata da dukkan 'ya'yana Wani mutumi daban ya bayyana cewa shima haka ya faru da shi kimanin shekaru goma da suka gabata lokacin da matarsa ta ce aurensu yazo karshe. 

Mijinta yace matarsa ta kwashe yara ta tafi da su gidan Fasto Harrison Anazodo Charles. Duk yunkurin da yayi na magance matsalar ta hanyar kai kara wajen yan sanda ya ci tura. Kai a karshe ma shi yan sanda suka daure. 

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN