Wani mutumi ya sayi gida da kudi N60m da aka tura masa cikin kuskure, yanzu Banki yace ya dawo da kudin


A ranar 29 ga Disamba, 2020, Russell Alexander, ya yi mamakin yadda aka fara tura masa kudi £110,000 (N60.7 million), cikin asusun bankinsa. Ba tare da bata lokaci ba ya garzaya Bankin Barclays dake Ingila domin sanar da su abinda ya faru.

Timesnow News ta ruwaito cewa bankin ta fadawa Russell ya tafi ya rike kudin saboda kudin gado be, ashe kuskure sukayi. 

Kawai sai Mr Russell ya garzaya kasuwa ya sayi makeken gida a watan Yuni, 2021. 

Banki tace ya dawo da kudin Bayan watanni tara, Bankin Barclays ya gano cewa kuskure akayi kuma ya umurce Mr Russell ya dawo da kudin. 

A cewar DailyMail, bankin yace lallai kuskure yayi wajen turawa Russell kudi kuma an sake tafka wani kuskuren wajen fada masa ya rike kudin. Bankin sun samu nasarar kwashe kudaden dake asusunsa saboda ya ajiye daidai kudi tare wasu yan canji ciki. 

Yanzu sun bashi kyautan £500 (N276k) ya rage zafi. Mutumin yace basu kyauta masa ba Mutumin wanda mazaunin Norfolk a Birtaniya ne yace bankin bai kyauta masa ba saboda sun bata masa tsarin rayuwa. 

Yace: "Na yi mamakin lokacin da kudin suka shigo, amma da na je banki har sau biyu nace su duba, sun ce in kashe kudin kawai."

 Source: Legit.ng 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN