Duba namijin da ke takarar kujerar shugabar mata ta APC a Najeriya da kuma dalilinsa


Ameer Sarkee mai shekara 26, wanda yake takarar kujerar shugabar mata a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa ya fito takarar ne domin namiji ne ya kamata ya riƙa lura da al'amuran mata a ko wanne lokaci.

Ameer ya taɓa tsayawa takarar kujerar shugabar mata a jam'iyyar PDP reshen jihar Kano a 2019 amma bai yi nasara ba, sai dai ya ce a wannan karon ba zai bari a kayar da shi ba saboda tun yana karamin yaro batutuwan da suka shafi mata ya fi son aiwatarwa.

"Tun ina ƙaramin yaro idan na ga mace tana buƙatar taimako nakan yi ƙoƙarin taimaka mata - kamar ɗaukar kaya ko sayo musu wani abu - kuma hakan ne ya sa nake son zama shugaban mata na jam'iyyarmu," a cewarsa.

"Wasu mutane suna tambayata abin da ya sa nake takarar kujerar shugabar mata kuma amsar da nake ba su ita ce 'Allah ya halicci namiji domin ya zama mai lura da lamuran mata'", in ji Ameer

Matashin dan asalin jihar Kano wanda ke sana'ar tufafi ya ƙara da cewa abin da yake ƙona masa rai shi ne yadda mata kan yo fitar-ɗango domin kaɗa ƙuri'a a lokutan zaɓe amma da zarar sun gama sai masu mulki su kawar da kai daga sha'anin ci gabansu.

Ya ƙara da cewa idan ya yi nasara zai tabbatar da ganin an ƙara jin muryoyin mata a sha'anin siyasa da mulki.

Dangane da ƙalubalen da yake fuskanta a takarar da yake yi, Ameer ya ce yana fatan matan jam'iyyar APC za su amince su zabe shi duk da yake shi namiji ne.

Ameer Sarkee
Bayanan hoto, Ameer ya ce yana fuskantar kalubale daga wrin matan da suke gani zai kwace musu mukami
"Babban ƙalubalen da nake fuskata shi ne samun amincewar mata, wasu suna kishin ganin na shugabance su, wasu kuma suna ganin zan kwace abin da yake nasu ne amma ba haka ba ne," a cewar Ameer.

Matashin dan siyasar ya ce: "A lokaci guda kuma ina samun ƙwarin gwiwa daga wurin mata, ko da a jiya sai da wasu kungiyoyin mata suka zo domin jaddada goyon baya a gare ni sannan da dama daga cikinsu suna goyon bayana a shafukan sada zumunta."

Duk da yunƙurin da Ameer yake yi domin ganin ya inganta lamuran mata, a halin yanzu ba shi da aure ko da yake cewa yana shirin angwancewa.

"Aure ba abu ne da ake gaggawar yi ba amma ina nan ina ci gaba da shirin angwancewa," in ji shi.

Ameer ya ƙara da cewa matakin da jam'iyyar adawa ta PDP ta dauka na zaben dan shekara 25 a matsayin shugaban matasanta ya nuna cewa yanzu lokaci ya yi da matasa za su karɓi jagorancin Najeriya.

Legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN