Yadda gobara ta kona jarirai hudu a Indiya


A kalla jarirai hudu ne suka mutu a wata gobara da ta tashi a dakin renon jarirai sabuwar haihuwa a jihar Madhya Pradesh da ke tsakiyar Indiya.

'Yan kwana-kwana sun yi nasarar kubutar da jarirai 36 daga asibitin yara na Kamla Nehru Children's Hospital da ke Bhopal da tsakar daren jiya.

Hotunan da sukai wadari a shafukan sada zumunta sun nuna yadda iyayae da 'yan uwan jariran ke tsaye a babbar kofar shiga asibitin cikin dimuwa da tashin hankali, wasu na kokarin dannawa ciki duk kuwa da yadda hayaki ya turnuke asibitin.

Kawo yanzu ba asan musabbabin tashin gobarar ba, sai dai jami'an na cewa ta yiwu wutar lantarki ce ta haddasa ta.

Ministan cikin gida Shivraj Singh Chouhan, ya bukaci a gudanar da binciken gaggawa kan musabbabin tashin gobarar, da kuma bukatar bai wa iyayen jariran da lamarin ya shafa diyya.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN