Kungiyar N/Delta ta fito, tana yi wa Gwamnan Arewa yakin zama Shugaban kasa a zaben 2023


Wata kungiyar magoya bayan 'yan siyasa mai suna Niger Delta Coalition for Gov. Bello 2023 da ta fito, tana goyon bayan gwamnan jihar Kogi a 2023.

Jaridar PM News tace kungiyar tana rokon gwamnan Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya bayyana niyyar tsayawa takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.

Kungiyar ta Neja-Delta ta fitar da jawabi ta bakin shugabanta, Sambo Temple, tana kira ga gwamnan na APC ya nemi babbar kujerar a zaben na 2023.

Kwamred Sambo Temple yace Niger Delta Coalition for Gov. Bello 2023 tana da mabiya a jihohi shida na yankin Neja-Delta da suke goyon bayan Yahaya Bello.

A jawabin da ya fitar, Punch ta rahoto Temple yana kira ga Bello, ya ceci kasar nan daga halin da ta shiga, ganin irin abubuwan a yaba da ya kawowa jihar Kogi.

Jawabin shugaban NDCGB 2023, Sambo Temple

“Kasar nan za ta kai ga ci ne a wannan tsari idan an samu shugaba mai taka-tsan-tsan, da ya san aiki, kuma mai gaskiya irin gwamna Yahaya Bello.”

“’Yan Najeriya na burin Yahaya Bello ya zama shugaban kasarsu, duba da irin gagaruman ayykan da ya yi wa jihar Kogi, za a so ya yi irinsu a kasa.”

“Muna bukatar Najeriya ta samu cigaba, ta zauna lafiya, kuma gwamna Bello shi ne wanda zai iya kai kasar nan ga ci.” - Kwamred Sambo Temple.

An dade ba a samu shugaban da ake buri ba

A jawabin na sa har ila yau, shugaban kungiyar NDCGB 2023 na kasan yace an dauki tsawon lokaci Najeriya ba ta samu irin shugaban da al’umma suke so ba.

Yahaya Bello a na sa ra’ayin shi ne zai cike wannan gibi, ya zama jagoran da ake nema ya mulki kasar nan, la’akari da yadda gwamnatinsa ta kawo cigaba a Kogi.

Gwamnan jihar Kogi zai yi takara a 2023?

Alamu na nuna Gwamnan na APC zai tsaya takarar kujerar Shugaban kasa. Kwanaki Gwamnan yace ya yi imani Bola Tinubu ba zai yi takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Da aka yi hira da shi, Bello yace matasa da mata da sauran ‘yan Najeriya na kiran shi ya fito takara, yace bai taba kashe ko sisi wajen buga allunan neman takara ba.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN