Yadda 'yan tawayen Kamaru suka 'kashe sarki da kona ƙauyuka' a Najeriya


Hallaka sarkin Manga da wasu mutum 10 da ake zargin mayakan 'yan awaren Kamaru wato 'yan Ambazonia suka yi ya haifar da zaman zullumi da fargaba tsakanin mazauna Karamar Hukumar Takum na Jihar Taraban Najeriya.

An shiga zaman makoki a kauyen Manga bayan kazamin harin da ake zargin mayakan da kaiwa da asubar Laraba a ƙauyen da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Bayanai sun ce har yanzu ana neman mutane da dama waɗanda ake zargin ko dai ɓata suka yi a cikin daji ko kuma maharan sun yi awon gaba da su.

Wannan yanayi da ake ciki ya tilasta wa Majalisar Dattijan Najeriya bukatar sojoji da sauran jami'an tsaro su tashi tsaye wajen kare martabar Najeriya daga hare-haren ƴan tawayen Kamaru.

Mataimakin shugaban marassa rinjaye a majalisar, Sanata Emmanuel Bwacha mai wakiltar Taraba ta Kudu ne ya gabatar da kudurin, yana cewa lamarin na bukatar a gaggauta daukar mataki.

'Cin fuska ga Najeriya'

Sanata Bwacha ya ce yanayin akwai tayar da hankali domin da safiyar Laraba suka kai harin da bude wuta kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, da kone kauyen kurmus.

Ya ce ba za a lamunci baƙi su shiga gari su aikata irin wannan ta'asa ba, kuma gane 'yan Ambazonia ba wahala ba ne tun da makwafta ne ana iya ganesu.

Ya ce tabbas 'yan Ambazonia ne suka kai wannan harin domin an gane su kuma sun bar shaida.

Sanatan ya kuma ce akwai takaici a ce su tsallako daga kasarsu, su shigo Najeriya da aikata wannan mummunar aika-aika, wannan ba abu ne da ba za a bari ya wuce ba, cin fuska ne ga ƙasar.

'Tilasta zaman gida'

Mai ba da shawara na musamman ga gwamnan jihar Taraba, Hon. Joseph Manga, kuma ɗan'uwa ga sarkin na Manga wanda 'yan Ambazoniyar suka hallaka ya shaida wa BBC hali da akuba da kauyukan kan iyaka da Kamaru ke ciki saboda fargabar 'yan awaren.

Hon Joseph ya ce mayakan sun shiga kauyen ne da misalin karfe 5:30 na asuba suka bude wuta kan mutane wasu na guduwa ana harbesu su fadi.

Mista Joseph ya ce sun tabbatar mayakan Ambazonia ne suka kawo musu hari, saboda 'yan awaren na yawaita aikata ayyukan ta'addanci irin na mayakan Boko Haram a yankunansu.

Ya ce: "Suna bin kauyuka da lalata amfanin gona da tilasta wa mutane zaman gida saboda fargaba, ana cikin wahala da kunci musamman mata da yara saboda 'yan awaren sun daidaita s.''

"Sun kona gidajen mutane da dukiyoyi, sun lalata gari baki ɗaya, a halin yanzu babu wanda ya san adadin mutanen da aka sace."

Barazanar hare-hare

Hon Joseph ya ce mayakan na kawo musu harin ne ta jirgin ruwa saboda a kauyen nasu akwai tafki.

Ya ce sukan ajiye jirgin a gaba, sai su karaso cikin garin da kafa su aikata ta'asa, sannan daga bisani su tsere.

Sai dai ya ce a halin yanzu jami'an tsaro sun isa garin.

Karin Haske

Wannan yanayi da kauyukan Taraba da suka hada iyaka da Kamaru ke ciki karin barazana ne kan lamuran tsaro da Najeriya ke fama da su.

Harin na zuwa ne adaidai lokacin da matsalar tsaron ke sake rincaɓewa a jihohin arewa maso gabashin Najeriya da ke fuskantar barazanar hare-haren mayakan Boko Haram da ISWAP.

Masu sharhi dai na ganin akwai bukatar gwamnati ta sake tashi tsaye domin tsayar da irin wadannan hare-hare, ganin a halin yanzu ba a gama kakkabe ko dakile batun 'yan bindiga da kungiyoyi masu ikirarin jihadi

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN