Ko rike atishawa na iya zama ajalin mutum ? Duba wannan bayani


Yadda atishawa takan zo wa mutum kwatsam ba shiri, wasu ke alaƙanta hakan da mugun abu ko ma kusa da mutuwa.

Likitoci sun ce atishawa wani yanayi ne da ke kare huhu a lokacin da wani abu da ba iska ba ke ƙoƙarin shiga.

Iska ce kawai aka yarda ta shiga cikin huhu - idan akwai wani abu da ya zo kusa da hanci wanda ba iska ba ne shi ita za ta yi kokarin fitar da shi da karfi, wanda hakan ke haifar da atishawa.

A wani cikakken bayani da ta wallafa game da atishawa Mujallar lafiya ta Healthline ta ce atishawa taimako ne ga jikin É—an Adam, kuma yawanci ba ta zama sanadin wata babbar matsala ga lafiya.

Mujallar ta ce atishawa hanya ce ta fitar da wasu abubuwa da ba su dace ba daga hanci ko makogaro. kuma takan zo da ƙarfi lokacin fitar da iska ba tare da mutum ya shirya ba.

Ɗaya daga cikin aikin hanci shi ne tsabtace iskar da muke shaƙa, wato tabbatar da ba datti ko wata cuta. Wani lokaci kuma datti zai iya shiga hanci ya zama matsala wadda kuma ke haddasa atishawa.

'Atishawa ƙanwar mutuwa'
Wasu na cewa atishawa ta fi kusa da mutuwa saboda yadda mutum ke fita hayyacinsa.

Amma likita ya ce magana ce kawai ake faÉ—i a likitance ba haka ba ne.

Ya ce atishawa kamar kariya ce ga lafiyar mutum amma sai jiki ya yi ƙoƙari ya fitar da karfi. "Ba batun mutuwa ba ne batun ƙarin lafiya ne."

"Ana fita hayyaci ne saboda maƙoshi yana rufewa cikin daƙiƙa amma da an yi atishawa sai ya buɗe."

"Ba a son wani abin da ba iska ba ya shiga shi ya sa wurin ke rufewa shi ya sa mutum yake ji kamar sheƙawa lahira zai yi," in ji Dr Manya.

Abin da ke sa mutum atishawa

Abubuwa da dama ne ke haddasa atishawa, kamar yadda Dr Celeb Manya kwararen likita a babban asibitin Gusau a jihar Zamfara ya bayyana.

Abubuwan sun haɗa da tsarin yanayin jikin mutum da cutuka kamar mura da shaƙar sinadarai kamar turare da sauransu.

Masu bincike a Jami'ar Saarland sun ce a binciken da suka gudanar wasu mutane sun ce sukan yi atishawa da zarar sun ci abinci sun ƙoshi.

Haka kuma wasu sun ce sha'awar jima'i ma tana saka su shiga yanayin atishawa.

Bisa ga yanayin jikin mutum- abin da bai dace da jiki ba sai ya sa mutum ya shiga damuwa yana atishawa sosai.

Likitan ya ce wasu yadda jikinsu yake ba ya son suna kusa da wasu abubuwa, kamar ƙura daga shara ko hayaƙi inda ake abinci ko ƙamshin wani abu wasu kuma daga dabbobi kamar mage da kaji idan sun kusance su, za su dinga atishawa - wasu kuma har Kyankyaso yana saka su atishawa.

Kun san illar rufe hanci da baki yayin atishawa?

Masana sun ce miyar kuka na ƙara wa mata ni'ima da ƙarfin mazakuta ga maza
Jinin Haila: Abubuwan da suka kamata ki sani kan al'ada da É—aukar ciki
Wani yakan yi atishawa a lokaci guda, wani kuma zai dinga yi da yawa a lokaci guda wanda ke nuna akwai matsala.

Sannan atishawa takan zo da ƙaiƙayin ido da makogaro wata kuma har da majina.

"Wanda zai yi so ɗaya bai ƙara ba, wannan ba damuwa ba ne amma wanda zai yi fiye da biyu ko uku - irin wannan akwai bukatar ya ga likita," in ji Dr Manya.

Ya ƙara da cewa akwai wasu nau'ukan atishawa da suka bambanta da wadanda aka fi yi kuma tsarinsu daban yake.

Kamar masu ninkaya suna da nasu nau'in atishawa da suke wanda wurin iska yake toshewa saboda ba a son ruwa ya shiga.

Ko riƙe atishawa na iya zama ajali

Mutane kan yi kokarin rike atishawa saboda tsarguwa a cikin jama'a ko wasu dalilai nasu.

Wasu kan buɗe baki iskar ta fita a hankali wasu kuma za su riƙe har atishawar ta tafi a hankali. Amma Likitoci sun ce ba a iya rike atishawa idan har ta zo.

Abu ne mai wuya riƙe atishawa ya zama sanadin ajalin mutu, kamar yadda likita ya bayyana.

Ko da yake Mujallar Lafiya ta Healthline ta ce duk da ba ta taɓa cin karo da rahotannin cewa atishawa ta kashe wani mutum ba amma ba za a ce ba zai yiwu mutum ya mutu ba sakamakon riƙe atishawa.

Ta ce matsalolin da za a iya samu sakamakon riƙe atishawa za su iya muni sosai, kamar matsalar ƙwaƙwalwa da fasa makogaro da matsalar huhu, waɗanda dukkaninsu za su iya munin da za su iya haifar da mutuwa.

A cewar Dr Manya, idan mutum ya rike atishawa ya hana wa kansa fitar da wata cutar da ya kamata ya fitar.

Ya ce abubuwan da ke sa mutum yin atishawa ƙanana ne da ba su da mummunar illa ga mutum, kamar kura sai idan masu ciwon asma. "Hana fitar da ƙanana ciwo zai iya haifar da babban ciwo"

Mujallar lafiya ta Healthline ta ce akwai aƙalla mutum ɗaya da ya taɓa fasa makogaronsa ta sanadin riƙe atishawa, wanda har ta kai ba ya iya magana ko haɗiye abinci.

Sauran matsalolin d riƙe atishawa ke haifarwa da mujallar ta bayyana sun haɗa da karya haƙarƙari da matsalar kunne da ido da hanci.

Ko zuciya na daina aiki yayin atishawa?

Lokacin da mutum yake atishawa likita ya ce mutum yana samun raguwar bugawar zuciya sannan jinin shi zai sauka.

Ya ce misali idan bugun zuciyar mutum ya kai sau 100 a minti daya - lokacin da za a yi atishawa zai sauka zuwa 90 ko 80, haka ma jinin mutum yana sauka.

Mujallar lafiya ta ce atishawa ba ta haifar da bugawar zuciya, illa kawai bugawar zuciyar na raguwa.

Atishawa kamar yadda likitoci suka bayyana hanya ce ta kariya ga lafiya, kuma yawancin lokaci riƙe atishawa ba ya haifar da wani mummunan abu da ya wuce ciwon kai da ciwon gaɓɓai, amma a wani lokacin riƙewa kan yi muni.

Abin da ya kamata shi ne mutum ya kauce wa abin da zai sa atishawa, kuma a bar jiki ya yi atishawa a lokacin da ya buƙata.

Rahotun BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN