Wata É—aliba dake koyon aikin jarida a kwalejin fasaha ta jihar Delta, Ogwashi-Uku, da aka fi sani da Chidimma ya daba wa saurayinta Daniel Johnson, wuka saboda yana fira da wata a WhatsApp.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ta daba wa saurayin wuka ne ranar Laraba 27 ga watan Oktoba, amma ya tsira daga lamarin.
Da yake bayyana halin da ya shiga bayan samun sauki, Johnson, yace budurwan tasa ta duba sakonnin shi na WhatsApp lokacin da yake bacci. Me budurwan da gani a WhatsApp É—in? A jawabina saurayin yace:
Ina bacci lokacin da ta É—auki wayana tana bincike, ta buÉ—e Whatsapp É—ina ta karanta hira ta da wata yarinya daban."
"Daga nan sai ta daɓa mun wuƙa a hannun dama, na tashi da yankar wuƙa a hannu na, na nemi mutane su taimaka mun kafin abun ya yi muni."
"Maƙota na ne suka cece ni, kuma aka kira yan sanda suka tafi da ita ofishin su na Asaba. Gaskiya na yi sa'a da na cigaba da rayuwa."
Wane mataki yan sanda suka ɗauka? Da aka tuntuɓe shi domin jin halin da ake ciki,
Kakakin yan sanda reshen jihar, DSP Bright Edafe, ya shaida wa manema labarai cewa har yanzun rahoton bai zo hedkwatar yan sanda ba.
Legit
Rubuta ra ayin ka