Kampanin WhatsApp ya sauya ka'idojin kiyaye sirri bayan tarar da aka ci kamfanin - isyaku.com


WhatsApp na sake sauya ƙa'idojin kiyaye sirri a sakamakon gagarumar tarar kare bayanai da aka ci kamfanin a farkon shekarar nan.

Sakamakon wani bincike ya sa wata hukumar kula da kiyaye bayanai ta ƙasar Ireland ta ci Whatsapp tarar fan miliyan 190 - wanda ita ce ta biyu mafi girma kan abin da ya shafi intanet - sannan hukumar ta bai wa Whatsapp umarnin sauya ƙa'idojin sirri.

WhatsApp na roƙon a ɗauke masa tarar, amma yana sauya bayanan ƙa'idojin nasa a Turai da Birtaniya don bin dokar.

Amma kuma kamfanin ya nanata cewa babu abin da ya sauya daga ainihin yadda yake gudanar da abubuwansa.

A maimakon haka, an yi sauye-sauyen ne don "ƙara bayanai kan ƙa'idojin da dama akwai su," kuma za a gansu ne kawai a tsari kiyaye sirri na Whatsapp din Turai, wanda dama can ya sha bambam da na sauran ƙasashen duniya.

A yayin da kamfanin ke anar da batun sauyin ya ce, "Babu wasu sauye-sauye kan yarjejeniyarmu da masu amfani da shafin, kuma ba za a buƙaci masu amfani da shafin su amince da wani abu ko yin wani abu ba don ci gaba da amfani da Whatsapp,"

Sabbin ƙa'idojin za su fara amfani ne ba tare da ɓata lokaci ba,

A watan Janairu, masu amfani da WhatsApp sun yi ƙorafi kan sabunta dokokin shafin da kamfanin ya yi, inda yawan mutane suka yi amannar cewa hakan zai sa a dinga aika bayanansu zuwa shafin Facebookk.

Da dama sun yi tsammanin cewa idan suka ƙi yarda da sabbin ƙa'idojin to za a toshe shafukansu. Sai dai a zahiri, abu ƙalilan ne ya sauta.

BBCHausa



Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN