Wani kyakkyawan matashi É—an kasar Brazil, Arthur O Urso, ya shiga
kundin tarihi na duniya bisa auren mata 9 a rana É—aya saboda soyayya.
Rahotanni sun bayyana cewa Angon kyakkyawa ne sosai abin kwatance, kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.
Meyasa Angon ya yi haka?
Mista Arthur ya bayyana cewa babban dalilinsa na yin haka shine don nuna tsantsar soyayya da kuma nuna adawa da auren mace É—aya tilo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan aure na mata 9 da kuma angonsu kwara ɗaya ya gudana ne a wata cocin Katolika dake garin Sao Paulo na ƙasar Brazil a nahiyar Latin America.
Kafin wannan aure, shin angon yana da mata?
Tun kafin É—aura wannan aure da ya kafa tarihi, Arthur yana da mata É—aya mai suna, Luana Kazaki.
Lokacin da suka fita yawon cin amarci tsakanin Arthur da amaryarsa ta farko Luana, suka yanke shawara kan cewa ya kara auren mata 9 su cika goma.
Ma'auratan sun amince da wannan matakin ne domin nuna wa duniya cewa soyayya ba ta mutum É—aya bace, ta kowa ce.
Rahotannin da aka tattaro a kafafen sada zumunta, sun tabbatar da cewa Arthur da Luana, sanannu ne a ɓangaren kwarewa a soyayya.
Kazalika ma'auratan sun yi Æ™aurin suna wajen yaÉ—a hotunan su na batsa yayin da sukehutun cin amarci a garin Cap D’Agde na Æ™asar Faransa.
Wannan birni ya shahara
Wannan birni dake ƙasar Faranta a yankin turawa, ya kasance makura a bariki, kuma har yanzun ana ta cece-kuce a kansa.
A garin dai an haramta yawo da kaya, hakan yasa Art
hur da Luana suka ci amarcin su a birnin kuma suna yawon buÉ—e ido babu tufafi a jikinsu.
Legit Hausa