Type Here to Get Search Results !

Duba wani bala'i da yan bindiga suka fuskanta a harin sojin sama a kauyukan Kaduna


Jami’an tsaron Najeriya sun sake samun galaba a kan wasu ‘yan bindiga a wasu hare-hare da suka kai a kewayen karamar hukumar Chikun. 

Inside Kaduna ta fitar da rahoto inda ta bayyana nasarar da sojojin suka samu a kan ‘yan bindigan. Jaridar ba ta iya bayyana adadin ‘yan bindigan da aka kashe daga luguden wutan da aka yi ba, amma an tabbatar da cewa an hallaka miyagu da-dama. 

Majiya daga gidan soja ta tabbatar da cewa an yi wa ‘yan bindiga rugu-rugu a kauyukan Kauwuri da Gaude, inda ake zargin bata-garin suna fakewa a nan. 

Binciken da jami’an tsaron suka yi da kuma bayanan sirri sun tabbatar akwai ‘yan bindiga da-dama da suke samun mafaka a yankin wadannan kauyuka. 

An yi lugude a Kauwuri da Gaude Rahoton yace a harin farko, jirgin yakin sojoji ya tarwatsa gungun ‘yan bindiga a garin Kauwuri. Sojoji sun hangi wasu ‘yan bindigan na tserewa daga yankin. 

Bayan nan sai aka tura wasu dakaru dauke manyan makamai a jirgin sama mai saukar ungulu, ya sauka kasa daf da jama’a domin tarwatsa ‘yan bindigan. An kai hari na biyun a Gaude bayan sojoji sun gano inda ‘yan bindigan suke boyewa. A nan ma an hangi miyagun suna neman boyewa a karkashin bishiyoyi. 

Samuel Aruwan ya fitar da jawabi 

Kamar yadda kwamishinan harkokin cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan ya bada sanarwa, daga nan ne sai aka yi wa wadannan miyagu luguden wuta. 

Legit Hausa

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies