Rundunar Yan sandan Najeriya a ranar Alhamis 10 ga watan Nuwamba, ta yi faratin mutum 16 da ake zargin sun kutsa gidan wata babban Jojin Kotun koli Mary Odili a birnin Abuja.
Kakakin rundunar na kasa CP Frank Mba ya yi faratin mutanen ga manema labarai a ofishin sashen binciken manyan laifuka na Criminal Investigations Department CID a birnin Abuja.
Ya ce wadanda aka kama sun hada da wani hafsan yansanda na bogi mai suna CSP Lawrence Ajojo da kuma wasu mutum bakwai da suka tsere.
Ya ce mutanen sun kutsa gidan Jojin ne bayan sun sami Labarin cewa Jojin ta aje makuddan kudaden daloli a gidanta.
Ya ce wadanda aka kama sun hada da wani tsohon Wakilin Jaridar Thisday Newspaper Stanley Nkwazema; da ma'aikatan Banki, Lauyoyi, Malaman tsibbu da Bokaye.
Domin samun labaran mu ta Whatsapp kai tsaye Latsa Link a kasa
https://chat.whatsapp.com/
Domin Tuntubar mu ko aiko Labari LATSA NAN
Domin zama Wakilinmu LATSA NAN
Shafin mu na Facebook facebook.com/isyakulabari
Shafin mu na Twitter twitter.com/isyakulabari
Rubuta ra ayin ka