Kano Tumbin Giwa: Ganduje ya dauka masu rawar koroso 45 aikin dindindin


A ranar Laraba da ta gabata, gwamnatin jihar Kano ta mika takardun daukar aikin dindindin ga masu rawar gargajiya wadanda aka fi sani da 'yan rawan koroso 45 a jihar.

Sabbin ma'aikatan rawan da aka dauka aiki an saka su a matsayin kananan ma'aikata ne wadanda za su yi aiki karkashin ma'aikatar tarihi da ofishin al'adu na jihar.

A yayin mika takardun daukar aikin a ma'aikatar, kwamishinan ma'aikatar al'adu, Ibrahim Ahmad Karaye, ya yi bayanin cewa wannan kyautatawar an yi ta ne domin karrama kananan ma'aikata masu aiki tukuru.

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, ya ce gwamnatin Ganduje ta mayar da hankali wurin saukake rayuwa tare da mayar da ita mai ma'ana ga jama'a ta hanyar kaddamar da ayyuka tare da shirye-shirye da ke taba rayukan jama'a kai tsaye tare da tabbatar da cigaban jihar.

Tun farko, sakataren ma'aikatar tarihi da ofishin al'ada, Ibrahim Umar Tofa, ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin kan daukar masu rawan aiiki da tayi.

A yayin jawabi a madadin wadanda aka dauka aikin, Abdulaziz Abubakar da Jimmai Dauda, sun sha alwashin yin duk abinda ya dace wurin habaka al'adun jihar, Daily Trust ta wallafa.

Ganduje ya dauka alarammomi 60 aiki don koyar da almajiran Kano


A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya amince da daukar malaman Qur’ani (Alarammomi) 60 a fadin makarantun Almajiranci 15 da ke jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar, Sanusi Kiru, a wani jawabi a ranar Talata, ya ce daukar malaman guda 60 a makarantun Almajiranci zai fara aiki ne nan take.

Ya bayyana cewa, “Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya amince da hakan biyo bayan wata wasika da hukumar makarantun Islamiyya ta jihar (KSQISMB) ta gabatar a ranar Litinin.

“Daukar wannan aiki ya sake nuna jajircewar gwamnan wajen kawar da bara a titi da kuma rashin ka’ida wajen kafa makarantun Qur’ani ba tare da samar da muhimman gine-gine da suka kamata ba."

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN