Da duminsa: An kama matar da ke kai wa yan bindigan Kebbi, Sokoto, Niger da sauran jihohi harsasai na bindigogin AK47 da sauran makamai


Rundunar Yan sandan jihar Zamfara ta kama wata Mata yar shekara 30 mai suna Fatima Lawali da kwaran harsashi 991 na bindiga kirar AK47.

Shafin isyaku.com ya samo cewa Kwamishinan yansandan jihar Zamfara CP Ayuba Elkanah, ya shaida wa manema labarai haka ranar Juma'a a Shelkwatar yan sandan jihar Zamfara da ke birnin Gusau.

Ya ce Fatima, Yar asalin garin Kaura Namoda, tana kan hanyarta ne na kai wa rikakken Dan bindigan nan mai suna Ado Aliero harsasan. 

Ya ce Fatima tana samar wa Yan bindigan jihohin Sokoto, Katsina,  Kaduna, Kebbi, Niger da Zamfara harsasai kafin Allah ya tona asirinta ranar 25 ga watan Nuwamba da karfe 8:30 na dare.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN