Ash sha: Uwargida ta kitsa sace kanta ta bukaci N50.000 kudin fansa a wajen mijinta, duba abin da ya biyo baya


Rundunar yansandan jihar Ekiti ta kama wata matar aure mai suna Sule Nana bayan ta kitsa sace kanta domin ta karbi N50.000 kudin fansa daga wajen mijinta.

Kakakin hukumar yansandan jihar Ekiti ASP Sunday Abutu ya sanarwa manema labarai ranar Laraba a Adi-Ekiti babban birnin jihar.

Ya ce yansanda sun sami kiran gaggawa daga Nana ranar 20 ga watan Nowamba cewa wasu mutane sun sace ta a dajin hanyar Ifaki-Oye-Ekiti kuma sun bukaci a basu N50. 000 kafin su sake ta.

Bayan yansanda sun shiga bincike ne sai suka gano cewa Nana ce ta sace kanta da kanta domin ta karbi kudin daga mijinta saboda wasu bukatunta.

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN